1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin ƙudin ƙasashen G8

May 19, 2007
https://p.dw.com/p/BuLI

Ministocin kuɗi na ƙasashen G8, sun kammalla zaman taron su a birnin Postdam na ƙasar Jamus.

Sanarwar ƙarshen taron,ta bayyana damuwa agame da hauhawar parashen ɗayan man petur a kasuwannin dunia.

A dangane da batun tantanawar al´ammuran kasuwanci a ƙungiyar cinikaya ta dunia, sun yi kira da babbar murya ga ɓangarori daban-daban, su gaggauata cimma yarjejeniya.

Minisocin kuɗi na ƙasashen G8, sun yi yabo na mussamman, ga shugaban bankin dunia mai barin gado Paul Wolfowitz, a game da ayyukan da ya gudanar a nahiyar Afrika.

Sannan sun sake ɗaukar alƙawarin kara bada talafi domin taimakawa Afrika ta hita daga ƙangin talauci.

Saidai sun gitta sharaɗin ƙasashen na Afrika, su daina karɓar rance, na ba digi daga ƙasashenkamar su Sin, wanda ke maiyar da hannu agogo baya, wajen cimma burin da aka sa gaba.

A tsawan kwanaki 2, na mahaurori, sun gabatar da shawarwari a kann ajendar da shugabanin G8, za su tantana, a taron ƙolin da zai haɗa su ,a nan ƙasar Jamus, a wata mai kamawa.