Taron ministoci akan batun nukiliya na Iran | Labarai | DW | 18.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron ministoci akan batun nukiliya na Iran

A yau ne ministocin harkokin wajen kasashe 6 zasu gana a birnin Moscow na kasar Rasha,a kokarinsu na nemo bakin zaren warware rikicin nukiliya na kasar Iran.

Kasar Rasha dai tace zata sake nanata kudirinta na ci gaba da nemo hanyoyin diplomasiya wajen magance wannan rikici,yayinda manyan jamian na kasashen Rasha Amurka,Sin,Jamus,Faransa da Burtaniya suke ganawa nan gaba a yau din nan.

A halin da ake ciki kuma shugaban kasar Iran Mahmud Ahmedinajad wajen bikin ranar soji ta kasar a yau ya bukaci rundunar sojin kasar data zauna cikin shirin kota kwana tare da samun fasahar zamani a ko da yaushe domin maida martani ga duk wata barazana daka iya tasowa.

Ya kuma bada tabbacin cewa,rundunar sojinsa na zaman lafiya ne da tsaro,saboda haka babu wata barazana ga kasashe makwabta,sai dai abokan gaba a cewarsa.