1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

TARON MDD DA SHUGABANIN AFRIKA A ACCRA.

July 29, 2004

Yunkurin shugabanin Afrika wajen warware rikicin kasar Ivory Coast,a karkashin jagorancin Majalisar dunkin duniya.

https://p.dw.com/p/Bvhh
Sakatare General na MDD Mr Kofi Annan.
Sakatare General na MDD Mr Kofi Annan.Hoto: AP

Shugabanin kasashen nahiyar Afrika a karkashin jagorancin Sakatare general na MDD Kofi Annan na wannan taro na yini biyu ne domin ganin yadda zaa kawo karshen rikicin fadace fadacen kabilanci dake addabar kasashen Ivory Coast da yankin Darfur dake yammacin Sudan.Ana kyau tata zaton cewa,Mr Annan zaifi mayar da hankali ne wajen tattauna hanyoyin warware rikicin mayakan larabawa,wadanda ake zargin gwamnatin Sudan da marawa baya wajen kisan kauyawa bakake tare da koransu daga matsugunnensu.

Ayayin wannan muhimmin taro na yini 2 da aka bude yau a Accra,babban birnin Ghana,ana kuma kyautata zaton cewa shugabanin nahiyar zasu tattauna rikicin kasar Ivory Coast mai arzikin Cocoa,inda yan tawayen arewacin kasar da na kudanci magoya bayan gwamnati ke cigaba da dauki ba dadi da juna.

Mai masaukin baki kuma shugaban Ghana John Kufour ,yace tattaunawan zai maida hankali ne wajen ganin cewa an komo hanyar sulhu kann rikicin na Ivory Coast da nufin gano bakin zaren warwareshi.

Taron na yau wanda ke gudana a asirce,ya samu halartan shugaba Laurent Gbagbo,tare da wakilan kungiyoyin adawa da juna.Ivory coast wadda ta jima da kasancewa jagora cikin harkokin tattali dana siyasa a yankin yammacin Afrika,ta fada rikicin juyin Mulki a shekarata 1999,kana bayan shekaru 3 kasar ta fada yakin basasa.

Ayayinda dakarun kiyaye zaman lafiya ma mdd suka taimaka wajen warware rikice rikicen kasashe dake makwabtaka da ita,yarjejeniyar sulhu da aka cimma wajen kafa gwamnatin hadin gwiwa ya kasa cimma wani tudun dafawa,wanda ke cigaba da barazana wa harkokin tsaro a wannan kasa.

A tattaunawan share fagen bude wannan taron a jiya,Mr Anna ya fadawa shugabannin dake halartan taron cewa yayi fata a wannan karon zaa cimma nasara kann wannan yunkuri da aka sanya gaba.Ana saran shugabanin kasashen Benin,Burkina Faso,Gabon,Mali,Niger,Nigeria,Sierra Leone,Afrka ta kudu da Togo zasu hade da shugaba Laurent Gbagbo na Ivory Coast wajen tattauna hanyoyi da zaa bin da kawo karshen rikicin,wanda Kofi Annan da hadin Gwiwan Shugaba Kufour na Ghana suka dauki nauyin gudanarwa a Hotel din La Palm,dake birnin Accra.

Shugaban yan tawaye Guillaume Soro,tare da tsohon shugaban kasa Henri Konan Bedie,da tsohon Prime minista Allassan Ouattara,na daga cikin wadanda aka gayyata zuwa taron na Accra.

Sakatare General na kungiyar ECOWAS Mohammed Ibn Chambas,yace sun lashi takobin ganin cewa wannan taron zai taka rawar gani wajen gano bakin zaren warware rikicin siyasar da ivory Coast ke ciki.

Majiyar Diplomasiyya gabannin bude taron sun tabbatar dacewa idan har shugaba Laurent Gbagbo ya gaza wajen sulhunta sabanin,zasu bawa mdd shawaran kakabawa gwamnatinsa takunkumi.

Yunkurin da Kungiyar ECOWAS tasha yi a baya na ganin cewa an cimma daidaituwa tsakanin bangarorin adawa da juna yaci tura.To sai dai babu tabbacin cewa taron zai tabo batun rikicin yankin Darfur dake yammacin Sudan.

A gobe jumaa ne ake saran kammala wannan muhimmin taro na shugabanin Afrika a karkashin Jagorancin MDD.

Zainab A M Abubakar.