1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron mdd akan yakar yaduwar makamai masu guba

Sakatare General na MDD Kofi Annan yayi kira ga kasashe 155 dake halartan taron sake nazarin taron da aka gudanar shekaru biyar a baya,dasu gaggauta daukan matakan kare kasashen duniya daga illolin makamai masu guba,tare da gargadin adangane da karuwan barazanar ayyukan tarzoma da cigaban da ake samu ta fannin fasaha.Mr Annan ya lura dacewa shekaru biyar da aka gudanar da taron a baya,inda aka watse baran baran,ana samun karuwar cigaban fasaha da kimiya,wadanda ke nufin cin moriya nan gaba,sai dai hakan a hannu guda kuma na barazana ga rayuwar biladama.Sakataren mdd yace yana alfahari da yadda kasashe suka duka tukuru wajen yakar ayyukan tarzoma da cututtuka,amma dole ne kuma su cigaba da hada kawunansa wajen gudanar ayyuka na kare alummomi,duk dacewa baya sa zaton zaa samu daidaito.