1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron MDD Akan Al'amuran Tsaro

October 26, 2004

A jiya litinin ne MDD ta kammala taronta karo na biyar akan al'amuran tsaro a birnin Bonn

https://p.dw.com/p/BvfB

Dan-Adam na fuskantar barazana game da makomarsa a bangarori dabam-dabam, kama daga cututtuka masu yaduwa a cikin hamzari zuwa ga matsaloli na yunwa da bannatar da kewayen dan-Adam da kuma keta haddinsa, sai kuma uwa-uba, yake-yake, wadanda suka zama ruwan dare a duniya. Abin tambaya a nan kuwa shi ne ta yaya za a billo wa wannan matsala ta tabarbarewar tsaro? Yawa-yawancin masana dai sun fi danganta maganar tsaron da yake-yake, kamar halin da ake ciki yanzu haka a kasar Iraki. Amma ba kasafai ba ne ake batu a game da sauran matsalolin da suka shafi makomar rayuwar dan-Adam, kamar yadda muka lissafta a can baya. Wani abin da ya taimaka aka dukufa akan matakai na soja shi ne hare-haren nan na 11 ga watan satumban shekara ta 2001. Amma fa yakin da aka gabatar kan kasar iraki mai tsinana kome wajen kyautata makomar tsaro a duniya ba, illa ma ya kara tsaurara al’amura, sannan barazanar ayyukan ta’adda ta dauki wani sabon salo, kamar yadda aka ji daga bakin Hans Blix, tsofon shugaban tawagar binciken makamai ta MDD a Iraki, inda ya kara da cewar:

Da yawa daga Musulmi masu matsakaicin ra’ayi suna kyamar manufofin Amurka da sauran kasashen yammaci sakamakon yakin Iraki kuma hakan na taimakawa wajen bunkasar ayyukan ta’adda.

Dalilin matakin kai farmaki kan kasar Iraki da Amurka ta dauka shi ne ikirarinta na cewar Irakin na mallakar muggan makamai na kare dangi. Amma fa a yau kowa da kowa ya san wannan ikirarin ba ya da madogara, sannan a daya bangaren an wayi gari duniya na cikin hali na dardar a game da yiwuwar fadawar ire-iren muggan makaman a hannun ‚yan ta’adda. Abin da zai taimaka a kawo karshen wannan barazana shi ne matsin lamba daga bangaren MDD akan kowace kasa da ta rika bin diddigin ‚yan ta’adda domin hana su mayar da harabarta wani dandalin shirya hare-harensu na ta’addanci. Duk kasar da tayi kunnen-uwar-shegu da wannan manufa majalisar zata amince da a kai mata farmaki, kamar yadda lamarin ya kasance dangane da Tabilan a kasar Afghanistan, a cewar Hans Blix. Wani muhimmin abu kuma shi ne samar da kusantar juna da hadin kai a tsakanin sassan duniya dabam-dabam bisa manufar kyautata huldodin tattalin arziki da sabunta fasahar rayawa. Kazalika da daukar matakai bai daya domin kare hakkin dan-Adam da tsaron lafiyar jama’a. Ta haka ne kawai za a cimma zaman lafiya mai dorewa a duniya baki daya.