1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron matasan Jamus da na Afirka a garin Wittenberg

YAHAYA AHMEDNovember 27, 2006

A ƙarshen makon da ya gabata, shugaban Horst Köhler na tarayyar Jamus, ya gayyaci matasa daga nan ƙasar da kuma nahiyar Afirka, zuwa wani taro a garin Wittenberg da ke gabashin Jamus, don share fagen wani taron ƙolin kuma, har ila yau dai tsakanin Jamus da shugabannin Afirka, wanda za a gudanar a birnin Accra a can ƙasar Ghana a cikin watan Janairu mai zuwa.

https://p.dw.com/p/BtxI
Shugaba Horst Köhler yayin wata ziyara a nahiyar Afirka.
Shugaba Horst Köhler yayin wata ziyara a nahiyar Afirka.Hoto: picture-alliance / dpa/dpaweb

Taron na garin Wittenberg na da muhimmanci ƙwarai a tarihince, saboda a nan ne kusan shekaru ɗari 5 da suka wuce, shahararren masanin addinin kiristan nan Martin Luther, ya gabatad da nazariyyarsa inda ya ƙalubalanci cocin katolika da ta yi wa kafofinta na wannan lokacin sauyi. Wannan kiran ne dai tushen sauye-sauyen da aka samu har suka haifad da ɗariƙar Protestant ta addinin kiristan. Burin shugaba Köhler na tarayyar Jamus game da kiran wannan taron, ba don samad da sauyi ba ne a fannoni addini a nahiyar Afirka. Abin da ya fi mai da hankali a kansa shi ne musayar ra’ayoyi tsakanin matasan Jamus da na nahiyar Afirka, don samad da wata ajanda ta bai ɗaya, a kan canje-canjen da ake bukata a fannonin siyasa da na tattalin arziki a nahiyar ta Afirka, wanda kuma za a gabatar wa taron ƙolin da za a yi a birnin Accra na ƙasar Ghana a tsakiyar watan Janairu mai zuwa.

Amma wasu ƙwararrun masana kan nahiyar Afirkan na ba da shawarar a sake tsarin wannan taron tun da wuri. Saboda a nasu ganin, ba za a taɓa cim ma adalci ba, idan taron zai dogara ne kan tsarin da aka saba da shi, na masu ba da taimako daga ƙasashen Yamma da masu karɓar taimako dada Afirka. Stefan Mair, wani shahararren masani na Cibiyar nazarin al’amuran ƙasa da ƙasa da tsaro ta nan Jamus, ya bayyana ra’ayinsa kan wannan batun ne kamar haka:-

„A nawa ganin dai, zai yi wuya a ce an cim ma daidaito, inda duk mahalarta taron za su tsaya kafaɗa da kafaɗa a matsayi ɗaya, idan aka bi tsarin da muke da shi yanzu na masu ba da taimakon daga Yamma da masu karɓansa daga Afirka. Idan dai da gaske ake, to kamata ya yi, a gudanad da taron a wajen da’irar ba da taimakon raya ƙasa, inda za a iya takalo jigogin da suka shafi tabbatad da tsaro, da tafiyad da kyakyawan mulki alal misali.“

Duk da hakan dai jami’in na da kyakyawar fata game da jigogin da matasan daga Jamus da nahiyar Afirka suka tattauna a kansu. Ban da dai batun kare muhalli da inganta harkokin ilimi, jigogin sun kuma ƙunshi batutuwan da suka shafi damawa da matasan wajen yanke muhimmman shawarwarin siyasa da kuma ɗaukan matakan shwao kan tashe-tashen hankulla da faɗace-faɗace da makamai da ke ɓarkewa a yankuna daban-daban na nahiyar ta Afirka. Kamar dai yadda ya bayyanar:-

„Waɗannan jigogin, musamman janyo matasan shiga cikin tattaunawar da za a yi, kan hanyoyin magance yaɗauwar tashe-tashen hankulla, su ne za su iya samad da yanayi inda ɓangarorin biyu za su iya kasancewa a matsayi ɗaya na tsayawa kafaɗa da kafaɗa da juna. Ina ganin kuma, shigad da matasan da za a yi, a taron ƙolin, na birnin Accra na da muhimmanci kwarai da gaske.“

Da yake yi wa taron matasan jawabi a garin Wittemberg, shugaban ƙasar Jamus Horst Köhler, shi ma ya nanata muhimmancin da akwai na janyo matasa da kuma ba su damar shiga cikin sharawarin zayyana wa nahiyar sabuwar alƙibla ta siyasa.

Farfesa Emmanuel Gyimah-Boadi, daga ƙasar Ghana, wanda shi ma aka gayyace shi halartar taron na Wittemberg, ya yabi irin ƙwazon da shugaban ƙasar Jamus Kohler ke nunawa wajen bunƙasa tafarkin dimukraɗiyya da harkokin siyasa a nahiyar Afirka. Muƙamin da ya riƙe a da can kafin zamowa shugaban ƙasar Jamus, inji Farfesa Boadi, wato na shugabancin Asusun Ba da Lamuni na Duniya, ya ba shi damar cuɗanya sosai da shugabannin ƙasashen Afirka da kuma fahimtar bukantunsu. Ya ƙara da cewa:-

„Bisa dukkan alamu dai shugabannin Afirka na nuna yarda ƙwarai da gaske ga shugaba Köhler. Wannan yardar kuwa, ita ce za ta iya sa a cim ma nasara a wannan fafutukar.“