1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron Majalisar Ministocin Cote D´ivoire

cewa……………………………..

Tun bayan girka sabuwar gwamnatin Cote D´Ivoire, a watan desember da ya wuce, a karro na farko, majalisar ministoci, ta yi zaman taro, da ya samu halartar ministoci baki ɗaya.

Wannan taro, da aka shirya, a fadar shugaban ƙasa Lauran Bagbo, ya samu halartar madugun yan tawaye Guillame Sorro, da ya dawo birnin Abija jiya, bayan fiye da shekara guda, da ya ƙauracewa gwamnati.

A cikin wannan sabuwar gwamnati, an damƙa masa, muƙamin ministan ministoci, mai kulla da ginin ƙasa, bugu da ƙari, mataimakin Praminista.

Yau kwanaki 100 daidai, da girka sabuwar gwamnatin, bisa jagorancin Charles Konnan banny, masu kulla da harakokinsiyasa a Cote D´ Ivoire, na nuni da cewar, wannan gwamnati, ta cencenci yabo, ta la´akari da yadda saban praministan, ya haɗa ɓangarori daban daban masu gaba da juna, watan da ya wuce a birnin Yamuskuro.

Sati 5 bayan wannan gagaramar haduwa, madugun yan tawaye ya dawo Abidja.

Ga kuma Allassane Watara, ya dawo daga gudun hijira.

A taƙaice ƙasar Cote D´Ivoire, ta kama hanyar samar da zaman lahia.