1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron majalisar kasashen larabawa

December 27, 2005
https://p.dw.com/p/BvEp

A yau ne majalaisar kasashen larabawa ta kaddamar da taronta na farko a birnin Alkhahira na Masar,sai dai jamian taron sunce zai dauki shekaru kafin majalisar ta samu karfin sauya harkoki ko kuma fada a ji cikin harkokin yankin.

Sakatare janar na kungiyar kasashen larabawa Amr Musa ya bude taron tare kuma da jawabi daga shugaba Hosni Mubarak na Masar ga Majalisar mai membobi 88,wadda hedkwatarta ke kasar Syria.

Mubarak yace samun hadin kai tsakanin kasashen larabawa,itace kadai hanya da zata basu damar fuskantar dukkan kalubale dake gabansu.

Kakakin Palasdinawa wajen taron,Rawhi Fattou,yace majalisar zatayi tasiri ne idan ta sanya ido sosai akan ababen da ke faruwa a gwamnatocin kasashen larabawa.

Kafa majalisar,wani bangare na shawarwari da Amr Musa ya baiwa kasashen larabawa domin karfafa kungiyar tasu.