Taron majalisar dokokin Iraq na farko ranar 12 ga wata | Labarai | DW | 06.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron majalisar dokokin Iraq na farko ranar 12 ga wata

Shugaban kasar Iraq Jalal Talabani yace zai kira taron farko na majalisar dokokin kasar a ranar 12 ga wannan wata da muke ciki,inda zai bukace su cikin kwanaki 60 su zabi Firaminista da ministoci na kasar.

Tashe tashen hankula na baya bayannan sun kawo jinkirin kafa sabuwar gwamnatin hadaka ta kasar da kuma yunkurin jaiyaun yan shia su ci gaba da rike Firaminista Al Jaafari a wannan matsayi.

Su dai shugabannin yan sunni da wasu Qurdawa sun nuna rashin gamsuwarsu da shugabancinsa na shekara guda a matsayin firaminstan rikon kwarya na Iraqi.