1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi

December 11, 2005
https://p.dw.com/p/BvH1

Babban taron MDD akan sauyin yanayi ya amince ya kara wa´adin yarjejeniyar birnin Kyoto akan rage dumamar doron kasa, bayan ta kare aiki a shekara ta 2012. Hakazalika taron wanda aka kammala jiya a birnin Montreal na kasar Kanada ya amince ya kaddamar da wata tattaunawa tsakanin kasashen da suka amince da yarjejeniyar Kyoto da kuma Amirka don daukar matakan na dogon lokaci da nufin rage fid da hayakin dake gurbata yanayi. Bayan cimma yarjejeniyar da ministocin kare muhalli daga kasashe 150 suka yi, ministan kare muhalli na Kanada Stephane Dion ya yabawa takwarorinsa. Har yanzu dai Amirka na adawa da yarjejeniyar birnin Kyoto.