Taron Majalisar Dinkin Duniya kan canjin yanayi a birnin Nairobi | Labarai | DW | 06.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron Majalisar Dinkin Duniya kan canjin yanayi a birnin Nairobi

Jami´an gwamnatoci da masana ilimin kimiyya da masu fafatukar kare muhalli daga ko-ina cikin duniya sun hallara a Kenya mai fama da matsalar fari, inda a yau za´a bude babban taron MDD akan sauyin yanayi. Wannan dai shi ne karon farko da za´a yi irin wannan taro a cikin wata kasa dake kudu da hamadar Sahara. Kawaunan kasashe 189 da suka sanya hannu kan yarjejeniyar kare muhalli a 1992 sun rabu zuwa gida biyu, yayin da kasashe 165 wadanda suka rattabawa yarjejeniyar Kyoto hannu a 1997 suka amince su rage fid da hayaki mai dumama yanayi, wasun kalilan ciki har da Amirka na ci-gaba da fatali da yarjejeniyar ta Kyoto.