Taron Majalisar dinkin duniya a kan Nukiliyar Iran | Siyasa | DW | 21.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron Majalisar dinkin duniya a kan Nukiliyar Iran

Kwamitin sulhun MDD zai yi muhawara a kan sabbin daftarin takunkumi da kasashen turai suka gabatar a akn Iran.

Shugaban Kasar Iran Mahmoud Ahmedinejad

Shugaban Kasar Iran Mahmoud Ahmedinejad

Kwamitin sulhu na majalisar ɗinkin duniya zai yi muhawar ce domin yanke shawarar ko zai amince da sabbin ƙudirin takunkumi a kan ƙasar Iran wanda ƙasashe masu zaunannun kujeru a majalisar ɗinkin duniyar suka cimma matsaya a kai ko kuwa zai amince ne da wasu kwaskwarima a daftarin ƙudirin.

A makon da ya gabata ne dai jakadun ƙasashen biyar masu wakilcin dundundun a kwamitin sulhun majalisar dinkin duniyar wadanda suka hada da Amurka da Britaniya da Faransa da Rasha da China tare da kasar Jamus suka cimma yarjejeniya a kan wasu jerin takunkumi waɗanda ke ƙunshe a cikin daftarin.

Shi dai wannan daftarin wanda ya tsananta matakan ladabtarwa a kan takunkumin da tun da farko majalisar dinkin duniyar ta sanyawa Iran a cikin watan Disambar bara, a makon da ya wuce aka gabatar da shi ga sauran ƙasashe goma waɗanda ba masu zaunannun kujeru ba a kwamitin sulhun domin jin raáyoyin su.

Taron na yau dai shine karo na farko da dukkan wakilai 15 a kwamitin sulhun za su sami damar musayar bayanai a game da abin da daftarin ya ƙunsa da kuma nazari a kan gyare gyaren da ƙasashen Afrika ta kudu da Qatar da kuma Indonesia suka bayar da shawara a kan su.

Bugu da ƙari wakilan kwamitin za kuma su yanke shawara a game da lokacin da ya dace a kaɗa kuriá a kan daftarin domin zartar da shi a matsayin doka, sai dai ƙasashen yammacin Turai na fatan kaɗa ƙuriár a cikin wannan makon.

A hannu guda kuma majalisar ɗinkin duniyar na shirin karbar baƙuncin shugaban ƙasar Iran Mahmoud Ahmedinejad wanda zai yiwa kwamitin sulhun jawabi a yayin da zata kaɗa ƙuriá a kan daftarin ƙudirin takunkumin. Tuni dai Washinton ta ce baiwa Ahmedinejad tare da muƙarraban sa Visa ta zuwa New York domin halartar taron majalisar ɗinkin duniyar.

Sabon daftarin takunkumin ya haramtawa Iran sayar da makamai zuwa ƙasashen ƙetare, kana ya kuma buƙaci ƙasashe bisa raɗin kan su kada su yi wata harkar kasuwanci da Iran. An kuma faɗaɗa jadawalin sunayen jamián gwamnatin Iran ɗin da kuma kamfanoni da zaá sanyawa takunkumin hada hadar kuɗaɗe da kuma fita zuwa ƙasashen waje.

Ƙasar Afrika ta kudu ta bayar da shawarar jinkirta takunkumin na watanni uku domin bada damar tattaunawa a tsakanin hukumar makamashin nukliyar ta IAEA da jamián sa ido na majalisar ɗinkin duniya a hannu guda kuma da mahukuntan Iran domin samun warware taƙaddamar cikin ruwan sanyi. Kasar ta Afrika ta kudu wadda ke rike da shugabancin kwamitin sulhun na wata guda har ila yau ta kuma gabatar da buƙatar wasu kwaskwarima a daftarin ƙudirin wanda ya haɗa da soke makamai da aka haramta da wasu tarnaƙi masu yawa ta hada hadar kudade.

Kasar Afrika ta kudu wadda ta kwance shirin ta na nukiliya a lokacin da take kokarin komawa kan tafarkin mulkin dimokradiya a tsakanin shekarun 1990 ta tsaya tsayin daka wajen kare yancin Iran na bunkasa makamashin Uranium ta hanyar lumana domin amfanin alumar ta.

Wani jakada na yammacin turai wanda ya bukaci kada a baiyana sunan sa, yace ƙasashen Qatar da Indonesia sun bada shawarwarin gyare gyare waɗanda ga alama sun fi karɓuwa ga yammacin turan fiye da shawarar Afrika ta kudu.

Ministan harkokin wajen Iran Manoucher Mouttaki ya tattauna ya gana da shugaban ƙasar Afrika ta kudu Thabo Mbeki a birnin Cape Town a game da taƙaddamar nukiliyar.

Ƙasashen yammacin turai dai na fargabar cewa Iran kokari na mallakar makamin kare dangi.