1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Majalisar alúma ta ƙasar Sin

March 6, 2007
https://p.dw.com/p/BuQS

Firimiyan ƙasar Sin Wen Jiabao ya buƙaci ƙasar ta rage abin da ya kira rashin ingancin cigaban tattalin arziki da dumbin amfani da makamashi. Firimiyan ya yi wannan waɗannan kalaman ne yayin da yake buɗe babban taron shekara na majalisar dokokin ƙasa Wen Jiabao yayi alkawarin ɗaukar matakan tsimin makamashi domin kare muhalli da kuma samun daidaito a yanayin rayuwar alúma. Shugabanin ƙasar mai bin tsarin kwamunisanci na ƙoƙarin ganin china ta rage dogaro a kan albarkatun mai daga ƙasashen ƙetare.