1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan kawar da hukuncin kisa a Geneva

February 24, 2010

Duk da cewar Majalisar Ɗinkin Duniya ta gabatar da kudurin dake kawar da hukuncin kisa tsakanin ƙasashe, har yanzu ana aiwatar da shi a wasu ƙasashe

https://p.dw.com/p/MA9w
Kisa ta hanyar ratayaHoto: BilderBox

A yau ne Majalisar Ɗinkin Duniya ta  kaddamar da taro na huɗu kan yaƙi da aiwatar da hukuncin kisa. Dubbanin masu fafutukar kare 'yancin bil'adama daga wakilan ƙasashe 192, ke halartan taron na birnin Geneva da aka fara tun a 2001.

Sama da shekaru 200 kenan shugabannin ƙungiyoyin fafutuka a Italiya   suka kaddamar da   kokarin kawar da hukuncin kisa a tsakanin al'umma, kamar yadda jakadar ƙasar  a Majalisar Ɗinkin Duniya Laura Mirachian ta tunatarwa da mahalarta taron...

"Italiya tana da dogon tarihi da daɗaɗɗiyar al'adar adawa da aiwatar da hukuncin kisa, wanda ya faro tun daga ƙarni na 18, lokacin da Toskana ya kasance birni na   farko da aka  dakatar da aiwatar da hukuncin kisa".

Indien Demonstration gegen Todesstrafe
Yaƙi da hukuncin kisaHoto: AP

Sai dai wannan birni na italiya a yau , bai  samu cimma wannan buri ba sai a shekara ta 1948. Shekarar da kuma zauren mashawartar Majalisar Ɗinkin Duniya ya amince da kudurin hukumar kare hakkin bil'adama na yin dokar da zata kawar da hukuncin kisa a hukumance. Duk da cewar ƙudurin batayi bayanin haramta hukuncin kisa a fili ba, sashi na uku na ƙudurin  ya bawa kowane mutun 'yancin rayuwa ba tare da tozarta ko gallaza masa ta kowace hanyar  mummunan hukunci ba.

A karkashin dokar kare hakkin bil'adama na shekara ta 1966 ne kuma, aka bukaci dukkan kasashe dake da wakilci a Majalisar dasu dakatar da aiwatar da hukuncin kisa, sai dai a yanayi na miyagun laifuffuka. Wannan shine karon farko da za'a iya cewar an cimma matsaya kan hukuncin, domin har zuwa wannan lokaci  hukuncin kisa na cigaba da kasancewa  a tarihin Duniya, tare da nuna halin ko oho a matakan ƙasa da ƙasa kan wannan batu. Kamar yadda kakakin wata ƙungiyar addini dake  fafutukar ganin an kawar da hukuncin kisa a Duniya na tsawon shekaru a birnin Saint Egidio, Mario Morazzitti ya tunatar...

" har ya zuwa shekarun 1970, ƙasashe 23 kawai ne suka soke aiwatar da hukuncin kisa"

To sai dai an samu cigaba sosai tsakanin kasashen duniya shekaru da dama bayan nan musamman a nahiyar turai, dangane da kawar da hukuncin kisa, kamar yadda Morazzitti yayi karin haske..

Symbolbild Todesstrafe Giftspritze
Hukuncin allurar kisaHoto: BilderBox

"A cikin shekaru 30 da suka gabata an samu sauyin alqibla, turai ta kasance nahiya ta farko a Duniya data dakatar da aiwatar ha hukuncin kisa"

 Wannan fafutukar dai ta faro ne daga Italiya zuwa nahiyar turai baki ɗaya, wadda  hukumar kare hakkin bil'adama  zuwa ga taron Majalisar Ɗinkin Duniya a Geneva ta kirkiro, domin tabbatar dacewar  babban zauren mashawartar Majalisar a birnin New York, ya amince da haramta aiwatar da hukuncin kisa a matakan kasa da kasa. Daga nan ne a shekara ta 1998 ,ƙasashen Turai ba tare da la'akari da adawar Amurka da Sin, dama wasu kasashen Asia da Afrika da akayiwa mulkin mallaka ba, suka gabatar da nasu kuduri.

"Morazzitti yace saboda akwai gagarumin adawa dake nuni dacewar, wannan tsohuwar akida ce ta mulkin mallakar 'yancin bil'adama, wadda keda matukar tasiri acikin gida"

Bayan gwagwarmaya na tsawon lokaci dai a shekarat ta 2007 ne, babban zauren mashawartar Majalisar Ɗinkin Duniya ya amince da kudurin dake kawar da aiwatar da hukuncin kisa.

Ƙasashe 141 ke darajawa wannan kuduri,93 daga cikinsun kuwa sun kafa dokar tabbatar da hakan. Ayayinda a 'yan shekaraun da suka gabata, an aiwatar da hukuncin kisa a kasashe  da suka haɗar da Amurka, Sin, Saudi Arabiya, Koriya ta Arewa da Iran.

Mawallafiya:Andreas Zumach/ Zainab Mohammed Edita: Abudullahi Tanko Bala