1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron mabiya addinin kirista ya yi ƙira ga kare muhalli.

May 13, 2010

Shugabannin kiristoci a Jamus sun bayyana wajibcin kula da muhalli

https://p.dw.com/p/NMyh
Hoto: picture alliance / dpa

Wani babban taron mabiya ɗariƙun kirista na cocin katolika da kuma Protestant dake gudana a birnin Munich na tarayyar Jamus, ya bayyana ajiye kowace ranar jumma'ar farko ta watan Satumba a matsayin ranar mayar da hankali ga batutuwan da suka shafi muhalli. Jagorar bishop - bishop na cocin Protestant a wajen taron Friedricht Weber ya sanar da cewar za'a sanya ranar a cikin jerin muhimman ranakun cocin domin bada fifiko ga matakan kare muhalli. Weber ya ƙara da cewar, cin gajiyar da ake yi ga albarkatun ƙasa ba tare da la'akari da abubuwan da zasu haifar a nan gaba ba, abin damuwa ne sosai.

Gabannin buɗe taron a wannan Larabar dai, shugaban mabiya ɗariƙar cocin katolika a nan Jamus Robert Zollitsch ya yi na'am da haɗin gwiwa wajen yin taron wanda kimanin mutane dubu 100 ke halarta. Taron zai ci gaba da gudana har ya zuwa ranar Lahadi - idan Allah ya kaimu, inda masu halarta za su taɓo batutuwa daban daban.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu