Taron mabiya ɗarikar Protestan a Cologne | Labarai | DW | 06.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron mabiya ɗarikar Protestan a Cologne

A yau a birnin Kolon a nan Jamus ake fara babban taro na 31 na mabiya addinin Kirista yan ɗarikar Protestant. Taron wanda Jamusawa kimanin 100,000 za su halarta zai kuma sami wakilcin baƙi 4,000 daga sassa daban daban na duniya. Shugaban Cocin Protestant a nan Jamus Bishop Wolfang Huber yace taron na kwanaki biyar zai kasance tsani ga taron ƙungiyar G8 a Heiligendamm da zai gudana a kusan lokaci guda. Muhimman batutuwan taron sun haɗa da haɗewar manufofin tattalin arzikin duniya da yaƙi da talauci da kuma musayar raáyi da fahimtar juna tsakanin Kirista da musulmi.