Taron MƊD akan yaki da gusowar Hamada a birnin Madrid | Labarai | DW | 15.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron MƊD akan yaki da gusowar Hamada a birnin Madrid

A birnin Madrid na kasar Spain, mahalarta babban taron MDD akan yaki da barazanar kwararar Hamada a duniya baki daya, sun amince da wani gagarumin shiri na tsawon shekaru 10 akan yaki da wannan masifa. To sai dai mahalarta taron daga kasashe 191 sun kasa cimma matsaya daya a dangane da ba da kudin tallafawa wannan shiri. A saboda haka MDD ta shirya yin wani zama na musamman a birnin New York a cikin mako mai zuwa. Kamar yadda ma´aikatar kare muhalli ta Spain ta nunar kasar Japan ce ta kawo cikas bisa manufa. Sanarwar ta ce saboda murabus din FM Shinzo Abe ya sa yanzu kasar Japan ba zata iya yanke hukunci ba.