Taron MƊD akan haƙƙin yara | Zamantakewa | DW | 14.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Taron MƊD akan haƙƙin yara

Yara na fuskantar muzantawa a sassa daban-daban na duniya da ake fama da rikici a cikinsu

default

Ana cin zarafin yara a wuraren rikici

Taron hukumar kula da manufofin haƙƙin ɗan-Adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin Geneva zai duba batutuwa da dama. Daga ciki kuwa har da haƙƙin samun kariya ga lafiyar yara, wanda a haƙiƙa abu ne dake ƙunshe a yarjejeniyar majalisar akan haƙƙin ɗan-Adam. Amma a zahiri lamarin ya banbanta, inda wasu yaran kan samu kansu a rikice-rikice ko kuma su taso a tskakkanin yaƙe-yaƙe.

A dai halin da ake ciki yanzu yara na samun wata 'yar ƙwarya-ƙwayar kariya game da ci da guminsu ko fuskantar barazana a wuraren da ake fama da yaƙe-yaƙe, kamar yadda aka ji daga bakin Rhadika Coomoraswamy, wakiliyar musamman ta Majalisar Ɗinkin Duniya akan haƙƙin yara a zauren taron hukumar majalisar akan haƙƙin ɗan-Adam a birnin Geneva:

"A shekarar da ta wuce an samu wani kyakkyawan ci gaba a sassa daban-daban na duniya game da taimakon yara a wuraren da ake fama da rikici. A ƙasar Nepal Majalisar Ɗinkin Duniya ta sa ido aka saki yara kimanin dubu uku daga sansanin soja. A yanzu Majalisar zata taimaka wa waɗannan yara wajen sake sajewa da sauran al'uma."

Kazalika wakiyar ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta lura da irin wannan nagartaccen ci gaba a yankunan da ake fama da rikici cikinsu a nahiyar Afirka:

"Ƙungiyar 'yantar da al'umar Sudan ta cimma yarjejeniya da Majalisar Ɗinkin Duniya ta kuma fara kakkaɓe hanuwanta daga sojoji yara. A Burundi ma tuni dakarun sa kai na ƙungiyar FML suka sallami sojoji yara ƙanana kuma jan aikin dake gaba a yanzun shi ne sake saje waɗannan yaran da sauran al'uma."

Amma fa wannan wani ɗan ƙaramin ci gaba ne aka samu bisa manufa domin kuwa har yau wajibi ne majalisar ta cike giɓin da take fama da shi ta kuma tinkari sauran ƙalubalen dake gabanta domin ba da kariya ga yara a wuraren da ake fama da rikici a cikinsu. An dai saurara daga Coomoraswamy tana mai ƙarin bayani da cewar:

Rotes Kreuz Ausstellung Genf

Matsalar fyaɗe a ƙasar Kongo

"Rahotannin baya-bayan nan game da fyaɗe a janhuriyar demoƙraɗiyar Kongo abu ne mai ban tsoro. Binciken da aka gudanar ya zuwa yanzu na nuni da cewar mata da yara kimanin 500 aka ci wa mutunci. Ɗaya daga cikin yaran ma bai zarce shekaru bakwai da haifuwa ba. Wannan babban alhaki ne da ya rataya a wuyanmu baki ɗaya."

Sai dai babbar matsalar dake akwai ita ce kasancewar ba a da wata kafa, wadda zata tilasta biyayya ga ƙa'idojin da aka shimfiɗa, musamman ma a ƙasashen dake da hannu a yarjejeniyar haƙƙin ɗan-Adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya. A sakamakon haka da yawa daga wakilan hukumar dake birnin Geneva suka bayyana goyan bayansu ga shawarar da Coomoraswamy ta bayar game da rashin tausaya wa duk wanda aka same shi da laifin cin zarafin yaran da ba su cika shekaru sha takwas da haifuwa ba. Ta kuma ce wajibi ne nan gaba a haramta ɗaukar yara 'yan ƙasa da shekaru sha takwas da haifuwa aikin sojan bauta wa ƙasa.

Mwallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu