Taron kyautata cude-ni-in-cude-ka a Jamus | Siyasa | DW | 12.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron kyautata cude-ni-in-cude-ka a Jamus

An yi taron kyautata cude-ni-in-cude-ka a Jamus tare da jagorancin shugabar gwamnati Angela Merkel

Shugabar gwamnati Merkel

Shugabar gwamnati Merkel

A lokacin taron wakilai sun amince da wani shirin da ya tanadi manufofin kyautata zama na cude-ni-in-cude-ka a harkoki na yau da kullum tsakanin Jamusawa da baki kimanin miliyan 15 dake Jamus. Sai dai kuma wasu kungiyoyi hudu na Turkawa sun kaurace wa taron na Berlin saboda bayyana adawarsu da manufofin karbar dangin ‘yan kaka-gida dake neman shigowa Jamus domin ci gaba da zama da ‘yan uwansu. An saurara daga kakakin kungiyoyin Kenan Kolat yana mai bayani a game da dalilinsu na kaurace wa taron, inda ya ce:

1.O-Ton Kolat

“Dalili shi ne dokar da aka gabatar ta kunshi wasu manufofi na wariya, wannan shi ne abin dake bata mana rai, muke kuma fushi da shi.”

To sai dai kuma ba wadannan kungiyoyin ne kadai ke adawa da sabuwar dokar ba, kazalika har da kungiyoyin kodago, kamar yadda aka ji daga bakin Annelie Buntenbach daga uwar-kungiyoyin Kodogon Jamus ta DGB:

2.O-Ton Butenbach

“Duk mai neman kyautata zaman cude-ni-in-cude-ka tsakani da Allah wajibi ne ya fara gabatar da matakai na shawarwari da tuntubar juna. Amma dokar da aka gabatar wani mataki ne na nuna kyama wanda ba shakka zai yi mummunar illa ga manufofin cude-ni-in-cude-kan.”

Duk da wannan korafi dai wakilai 90 na kungiyoyi daban-daban sun amince da wani shirin da shugabar gwamnati Angela Merkel ta gabatar akan kyautata zama na cude-ni-in-cude-ka, wanda kuma gwamnati ke fatan kashe abin da ya kai Euro miliyan 750 wajen wanzar da shi a cikin shekaru hudu masu zuwa. Sai da aka yi tsawon watanni da dama kafofi daban-daban da aka nada a wawware kama daga matsayi na gwamnati zuwa ga kananan hukumomi da ‘yan kasuwa da masu wasan motsa jiki suna musayar ra’ayoyi akan kudurorin da shirin ya tanada, wanda ya hada da inganta matakan koyar da Jamusanci ga ‘yan kaka-gida da samarwa da ‘ya’yansu wuraren koyan sana’o’i na hannu da ba su damar taka rawar gani a gidajen telebijin da kafofi na gwamnati da kuma kara karfafa ‘yancin mata. Merke ta ce:

3.O-Ton Merkel

“Wannan martani ne aka mayar akan halin da muke ciki a nan kasar dake kunshe da mutane sama da miliyan 15 dake da nasaba da kaka-gida. Wasu daga cikinsu sun saje ana damawa dasu a harkokin rayuwa ta yau da kullum a yayinda wasunsu kuma ke fama da matsala. Ba za a dadara da hakan ba. Wajibi ne kowane mahaluki dake nan kasar ya samu cikakkiyar dama da neman ilimi da kyautata makomar rayuwarsa.”

Merkel dai ta bayyana mamakinta a game da kungiyoyin Turkawan da suka kaurace wa taron kolin, tana mai bayyana fatan cewar zasu sauya tunani su halarci taron koli na gaba da za a gudanar a shekara ta 2008, inda za a yi bitar sakamakon da aka samu dangane da shirin da ta gabatar.