Taron kurraru da ministocin lahiyar dabbobi na Afrika a Rwanda | Labarai | DW | 31.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kurraru da ministocin lahiyar dabbobi na Afrika a Rwanda

Nan gaba a yau ne kurraru ta fannin lahiyar dabbobi na kasashenAfrika, za su fara zaman taro a birnin Kigali na kasar Rwanda.

A na shirya makamancin wannan taro ko wace shekara 3.

A tsawan kwanaki 5, mahalarta taron za su tantana batutuwa da su ka jibanci lahiyar dabbobi a Afrika.

Ministan albarkatun dabbobi na Rwanda, ya sannar cewa za su anfani da wannan dama, domin masanyar ra´ayoyi a game da cutar massara kaji da a halin yanzu ta dauki hankullan kasashen dunia.

A na sa ran su dauki mataki na bai daya, domin fuskantar wannan cuta.

Kasar Rwanda tare da wasu kasashe na nahiyar Afrika , tunni! sun dauki mattakan hana shigowa da kaji daga ketare domin riga kafi ga cutar.

Taron na birnin Kigali zai samu halaratar wakilan kungiyoyin kasa da kasa, daga Amurika da Turai.