1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kungiyoyi masu zaman kansu a Wagadugu

Yahouza sadissouSeptember 13, 2005
https://p.dw.com/p/BvZj

A birnin Wagadugu na Burkina Fasso, a na ci gaba da zaman taron kungiyoyi masu zaman kansu, na kasashen dake anfani da halshen fransanci.

Jiya ne a ka fara wannan taro bisa jagoranci shugaban hukumrar gamayar kasashe masu anfani da wannan halshe, bugu da kari tsofan shugaban kasar Senegal, Abdu Diuf.

Wannan shine taro na kasa da kasa, irin sa, na 5 da hukumar OIT wato, Organisation International de la Francophonie , ta shirya, tare da kungiyoyi masu zaman kansu ,na kasashe 53 membobin ta.

Kimanin wakilai 200 ne, daga sassa daban daban na dunia ke halartar taron, inda su ke tantana batutuwan, da su ka shafi yawnin da ya rataya a kann, kungiyoyin masu zaman kansu, a cigaban al´umma.

A yayin da ya ke jawabin sa, na bude taro, Abdu Diuf ya bayana mahimanci wannan kungiyoyi ta fannin waye kan jama´a, da kuma inganta rayuwa.

Yayi yabo na mussaman, a game da rawar da su ka taka, a fannoni daban daban, domin kyawttata rayuwar jama´a.

A sakamakon wannan kokarin, shugaban kungiyar OIT, ya tabatar wa mahalara taron cewa, hukumar da ya ke jagoranta a shire ta ke, domin ta kara damawa da su, a dukan ayyukan ta, na ci gaban jama´a.

A daya hannun ma, Abdu Diuf, ya shaida cewa, taron kungiyoyi nesa ba kusa ba, ya zarta taron shuwagabanin kasashe, inda saidai a taru a waste, ba tare da anyi anfani ba, da matakan da a ka tsaida.

A tsawan kwanaki 2 mahalarta taron na Wagadugu, za su masanyar ra´ayoyi a game da mahiaman batutuwa guda 4.

Na farko za su, mahaura a kan shi kansa halshen na Fransaci da kuma yadda ya kulla cudeni in cune ka, da soyyayya tsakanin dukan masu anfani da shi, tare da kiyyaye al´adu da hakkokin juna, a dukan kasashe membobin kungiyar Francophonie.

A mataki na gaba, akwai maharori a game da batun karffafa demokradiya da kiyaye hakkokin bani adama, sannan da maganar illimi da horo, sai kuma daga karshe hanyoyin cigaban kasashen.

A gaba daya, kungiyar kasashe masu anfani da halshen Fransanci, na aiki kafada da kafada, da kungiyoyi masu zaman kansu 63 .

Wannan kungiyoyi na aiki a cikin karkara da birane ta fannoni daban dabann na kwattata rayuwar bani adama.

Kazalika su na aikin a fadi dukan kasashe 53 na Francophonie, wanda su ka kunshi jamaá fiye da million dari 5.

Nan gaba a yau ne, a ke sa ran kawo karshen wannan taro.