Taron kungiyar tarayyar turai | Labarai | DW | 22.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kungiyar tarayyar turai

A birnin Brussels din kasar Belgium,shugabannin kungiyar tarayyar turai na cigaba da taron kolinsu ,inda shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel wadda kasarta ce ke rike da zagayen jagorancin kungiyar,take kokarin ganin cewa an cimma amincewa da yarjejeniyar kawo sauyi tsakanin wakilan kasashe 27 dake kungiyar.Merkel tayi baynin cewa cimma wannan yarjejeniya zai taimaka wajen ,saukaka yadda zaa rika tafiyar da harkokin wannan kungiya.Kasashen Britania da janhuriyar Czech da Netherlands da Poland dai sun bayyana adawansu da wannan yarjejeniya.Wannan yarjejeniya dai na wakiltar kundun tsarin mulkin kungiyar ne,wanda kasashen faransa da Holland suka jefa kuriar kin amincewa da ita shekaru biyu da suka gabata.