Taron kungiyar SADC | Siyasa | DW | 18.08.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron kungiyar SADC

Yau ne shugabanin kasashen yankin kudancin Afrika na kungiyar SADC ke kammala zaman taro a Gaborone

Shuwagabanin kungiyar habaka tattalin arzikin kasashen kudancin Afrika, wato SADC, na ci gaba da zaman taro a Gaborone babban birnin Botsawana.

Mahimman batutuwan da su ke tantanawa,a wannan haduwa, da ta yi daidai da cikon shekaru 25, da girka kungiyar, sun jibanci bullo da kudaden bai daya, nan da shekara ta 2020, ta yada SADC, zata kasance wani dandali, na bunkasa tattalin arzikin kasashe membobinta, da kuma kyawttata rayuwar al´ummomin su.

Shugaban kasar Botsuwana mai masaukin baki Festus Mogae, ya yi bitar nasarorin da kungiyar SADC ta cimma, bayan shekaru 25 da aka girka ta, da kuma akasi daban daban da su ka hana ruwa gudu, ta fanin cimma illahirin burin da aka sa gaba.

Ya ce kungiyar ta samu gagaramar nasara idan aka yi la´akari da kyawakyawar rawa da ta taka, ta fannin kwantar da ringinmun tawaye da na siyasa, da su ka barke, a cikin wasu daga kasashe membobin ta.

Haka zalika, ta fannin bunkasa tattalin arzikin duk da cewa ba a kai ban matsayin da aka bukatan, an samu nasarori da dama, duk da kasancewar, a yan shekarun baya bayan nan, alamomi na nuna sanhi sanhi ga huldodin cinikaya da cude ni in cude ka,tsakanin kasashen kudancin Afrika.

Daga manyan matsalolin siyasa, da kungiyar SADC ke fuskanta a halin yanzu, akwai rikicin kasar Zimbawe, da ya ki ci ya ki cenwa, tsakanin Robert mugabe da yan adawa.

A daya hanun kuma, kungiyar ta kasa tabuka komai, domin ciyo kan shugaba Robert Mugabe na ya dakatar, da ruguza gidajen talakawa, matakin da ya samu su ka daga kasashen ketare.

Shuwagabanin kasashen SADC, sun yi anfani da wannan taro, inda su ka yi kira da babbar murya, ga kasashen dunia, masu hannu da shuni, da kuma kungiyoyin bada agaji, na kasa da kasa, da su kayo taimakon gaggawa ga al´ummomin kasashen kudancin Afrika, kimanin million 10, da halin yanzu ke fuskantar barazanar fadawa cikin yanayin matasanaciyar yinwa.

Shugaban Botsawana, yayi kira ga takwarorin sa, na SADC da su gama karfi, da hussa´o´i domin bullo da mataikai, na dakile matsalar yinwa, kamin samun tallafi daga ketare.

Sannan kalubalen da ke gaban kungiyar inji shugaba Festus Moge, shine na nemo hanyoyin warware matasalar karancin ruwan sama, da ke shirin zama tubalin kara tabarbarewa rayuwa a wanan yankina Afrika.

A wani lokaci ne a yau, za a kammala wannan taro.

Kungiyar SADC ,ta kunshi kasashe 14, inda aka hada da Madagaskar, da kuma jimmilar yawan jama´a kimanin million dari 2.

A farkon girka kungiyar, a shekara 1980 ta na da kasashe 9,wanda a lokacin baban burin su, shine na tallafawa kasar Zimbabwe da ta samu yancin kai a wanan shekara, domin ta rage dogaro da Afrika ta kudu.

 • Kwanan wata 18.08.2005
 • Mawallafi Yahouza sadissou
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvaO
 • Kwanan wata 18.08.2005
 • Mawallafi Yahouza sadissou
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvaO