Taron kungiyar kasashen larabawa a Sudan | Labarai | DW | 28.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kungiyar kasashen larabawa a Sudan

Taron shugabannin kungiyar kasashen larabawa dake gudana a Khartoum babban birnin kasar Sudan, ya yi tayin tattaunawar zaman lafiya da Israila. Mahalarta taron wadanda suka soki lamirin rage tallafin kudi ga hukumar gudanarwar Palasdinawa karkashin jagorancin Hamas sun kuma bada shawarar komawa kann daftarin zaman lafiya tare da mashawarta na kasa da kasa domin cimma sulhu a tsakanin Israila da Palasdinawa. Rahotanni sun baiyana cewa shugabannin kasashe 12 ne kawai suka sami halartar taron. Da dama daga cikin manyan kasashen larabawan masu fada a ji suk kauracewa taron a sabili da shaánin tsaro da kuma kasancewar kasar Sudan na cikin wani hali na tsaka mai wuya da hukumomi na kasa da kasa a game da rikicin yankin Dafur.