1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Kungiyar AU a Ghana

June 29, 2007
https://p.dw.com/p/BuHe

A yau kungiyar gamaiyar Afrika ke fara babban taron ta a Ghana inda shugabanin kasashen za su tattauna a game da makomar kungiyar. Shugaban ta na farko, kuma marigayi tsohon shugaban kasar Ghana Kwame Nkurma ya yi nuni da cewa nahiyar ta Afrika zata cigaba ne kawai idan ta kasance nahiya daya dunkulalliya. shugaban kasar Ghana John Kufour da shugaba Gadhafi na Libya na masu raáyin gaba dai gaba dai na kafa hadaddiyar daula ta kasashen tarayya Afrika. Shugabanin kasashen 53 na Afrika za kuma su tattauna batutuwa da suka shafi aikin wanzar da zaman lafiya a kasashen Somalia da kuma yankin Dafur na kasar Sudan.