Taron Komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia a kan kasar Syria. | Labarai | DW | 31.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron Komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia a kan kasar Syria.

Nan gaba a yau ne ministocin harakokin ketare na kasashe membobin komitin sulhu na Majalisar Dinkin dunia za su zaman taron domin tantanawa a kan batun daukar matakan hukuta kasar Syria, da a ke tuhuma da rashin bada hadin kai ga bincike a kann mutuwar tsofan Praministan Labanon Raffik Hariri.

Kasashehn Amurika Fransa da Britania ne, su ka bayyana bukatar daukar matakan cilastawa Syria ta bada hadin kai, ta fannin saka mata takukumin karya tattalin arziki, da kuma mayar da ita saniyar ware, a fagen diplomatia na kasashen dunia.

Hukumomin Syria sun yi suka ga wannan mataki da su ka kira na rashin adalci, da a ke shirin dauka a kan su, sun kuma bayyana kafa wani komiti na daban domin bincikar al´amarin.