Taron Kolin Shuagabannin KTT a Brussels | Siyasa | DW | 16.06.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron Kolin Shuagabannin KTT a Brussels

A gobe alhamis idan Allah Ya kaimu shuagabannin kasashen KTT zasu fara taron kolinsu na yini biyu a Brussels domin neman cimma daidaituwa akan kundin tsarin mulki bai daya tsakanin kasashen kungiyar

Shelkwatar Kungiyar Tarayyar Turai (KTT) a Brussels

Shelkwatar Kungiyar Tarayyar Turai (KTT) a Brussels

Bisa ga ra’ayin gwamnati a fadar mulki ta Berlin, a inda take kasa tana dabo shi ne kasancewar ko da yake kusan dukkan kasashen kungiyar sun amince da shawarar ta tagwayen kuri’a daidai da yawan al’umar kasa, amma za a sha fama da wahala wajen wanzar da wannan kuduri. Da farkon fari dai kasashen Spain da Poland sun bayyana adawarsu da wannan shawara, amma sai suka janye daga wannan matsayi nasu kuma ba abin da ya rage illa a zayyana sibgar wanzar da ita. Shawarar da gwamnati a fadar mulki ta Berlin ta bayar, wacce kuma kasar Irland dake shugabancin Kungiyar Tarayyar Turai a halin yanzu zata gabatar da ita domin tattaunawa a zauren taron kolin na yini biyu a Brussels, shi ne rinjayen kashi 55% na kuri’un da za a kada akan wani kuduri na kungiyar, idan har kasashen da suka ba da wannan goyan baya yawan al’ummomin ya kai kashi 65% na illahirin al’umar kasashen KTT. To sai dai kuma gwamnatin ta Jamus ba ta gamsu da daya shawarar da ake nema da a gabatar da ita a zauren taron kolin ba, wacce ta tanadi hana wanzuwar duk wani kudurin da za a gabatar idan har an fuskanci adawa daga kasashe hudu na kungiyar ko kuma kasashen da idan sun hadu a karkashin laima guda yawan al’umarsu zai kai kashi 15% na illahirin al’umar Kungiyar ta Tarayyar Turai. Kazalika gwamnati na adawa da daya shawarar wacce ke cewar bai kamata nan gaba a rika shigar da masu rowar kuri’unsu a cikin lissafi ba. A ganinta wannan mataki zai kara haifar da rudami ne a tsarin kuri'ar raba gardama akan kudurorin kungiyar. Fargabar da gwamnati ke yi game da haka shi ne ka da a kai ga wanzar da wani kuduri, wanda ba a cimma wani takamaiman sakamako na goyan baya ko kin goyan bayansa ba. Daya matsalar kuwa ta shafi bangarori ne da suka shafi manufofin haraji da zamantakewar jama’a, wadanda ake fama da sabani kansu a karkashin daftarin tsarin mulki bai daya da ake da niyyar gabatarwa tsakanin kasashen kungiyar tarayyar Turai. A wannan bangaren gwamnatin Jamus zata ba da cikakken goyan baya ga kudurin mafiya rinjaye ta yadda ba za a samu wasu tsiraru da zasu nemi hana ruwa gudu akan manufa ba. Dangane da sabon shugaban da za a nada domin shugabancin hukumar zartaswa ta kungiyar kuwa Jamus na sha’awar ganin an tsayar da P/M Belgium Mr. Guy ne domin ya maye gurbin Romano Prodi mai barin gado. A game da danganta daftarin da wata manufa ta addini kuwa ba bu wata alamar dake nuna samun kusantar juna tsakanin kasashen kungiyar ta tarayyar Turai a wannan marra da ake ciki yanzun. To sai dai kuma hakan ba zai hana ruwa gudu wajen cimma daidaituwa domin wanzar da daftarin tsarin mulkin bai daya tsakanin kasashen na Turai ba.