1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kolin shuagabannin KTT a Brussels

June 17, 2005

A taron kolinsu a birnin Brussels, shuagabannin KTT sun mayar da hankalinsu ne kacokam akan yawan kudin da za a kasafta wa kungiyar daga 2007 zuwa 2013

https://p.dw.com/p/BvbG

A dai halin da ake ciki yanzu KTT ta ajiye maganar daftarin tsarin mulki a gefe guda. Dalili kuwa shi ne, shuagabannin kasashen kungiyar dake gudanar da taron kolinsu Brussels yanzu haka, basa kaunar sake jefa kansu da kansu a cikin wani sabon garari sakamakon fatali da kudin tsarin mulkin da al’umar kasashen Faransa da Netherlands suka yi. A cikin wani bayani da yayi P/M kasar Luxemburg Jean-Claude Juncker dake shugabancin kungiyar yanzu ya ce da wuya a cimma wa’adin watan nuwamban shekara ta 2006 da aka tsayar da farko domin amanna da daftarin tsarin mulkin. Za a ba wa kowace kasa cikakkiyar dama ta sararawa domin tunani ko Ya-Allah zata albarkaci kundin ko kuwa zata yi fatali ne da shi. To sai dai kuma Juncker ya kara da bayani yana mai jaddada cewar:

Wajibi ne a ci gaba da hada-hadar neman amincewa da daftarin tsarin mulkin, saboda babu wani zabi a’ala akan abin da wannan kundin ya kunsa kuma a sakamakon haka maganar sake shawartawa kansa ba ta taso ba. Dukkan kasashen da suka albarkaci kundin da kuma wadanda ke da niyyar kada kuri’ar raba gardama kansa suna da isasshen lokaci na tunani da mahawara da kuma wayar da jama’a game da shi.

A baya ga kasar Birtaniya, su ma kasashen Denmark da Portugal sun dakatar da shawararsu ta kada kuri’ar raba gardama akan daftarin tsarin mulkin bai daya tsakanin kasashen KTT. Ita ma kasar Chek tana shawarar bin sau. Wata maganar dake da dangantaka ta kut-da-kut da batun daftarin tsarin mulkin kuma ita ce dangane da karbar karin kasashe a Kungiyar ta Tarayyar Turai. Juncker dai ya fito fili ya bayyana cewar ba za a sake mayar da hannun agogo baya ba, kungiyar zata ci gaba akan alkawarinta dangane da kasashen Rumaniya da Bulgeriya. Kazalika wannan maganar ta shafi har da Turkiyya, inda za a cika alkawarin fara shawarwarin karbarta a kamar yadda akasarin kasashen kungiyar ke tattare da ra’ayi. A zamansu na yau juma’a shuagabannin na fatan cimma daidaituwa akan takaddamar da ake famar kai ruwa-rana kanta a game da abin da za a kasafta wa kungiyar daga shekara ta 2007 zuwa shekara ta 2013. Ga alamu dai da wuya a cimma wata manufa mai sassauci da zata gamsar da dukkan bangarorin da lamarin ya shafa, kamar yadda aka ji daga bakin shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder, inda yake cewar:

Jamus na fatan ganin an cimma daidaituwa, kuma kasar a shirye take ta yi sassauci iya gwargwado, amma fa tilas ne dukkan bangarorin da lamarin ya shafa su nuna halin sanin ya kamata akan wannan batu. Ko da yake ina fatan hakan, amma wajibi ne a yi taka tsantsan.

Kasar Birtaniya dai har yau tana ci gaba da taurin kai tare da dagewa akan rangwamen kudadden gudummawar da ake yi mata tun misalin shekaru 21 da suka wuce. Kazalika kasar Faransa ba ta so ta janye daga taimakon kashi daya bisa biyar da take samu daga asusun karyar farashin amfanin noma na kungiyar da ya tanadi Euro miliyan dubu 40.