1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kolin shuagabannin KTT a Brussels

June 20, 2005

Taron kolin shuagabannin KTT ya ci tura

https://p.dw.com/p/BvbE
Ba a cimma daidaituwar kasafin kudin KTT ba
Ba a cimma daidaituwar kasafin kudin KTT baHoto: dpa - Fotoreport

A ranar asabar da sanyin safiya an ji P/M kasar Luxemburg dake shugabancin kungiyar tarayyar Turai yana mai bayanin cewar kungiyar na cikin mawuyacin hali na kaka-nika-yi. Wasu daga cikin kasashenta na ci gaba da nuna taurin kai da hana ruwa gudu wajen cimma daidaituwa akan manufa, saboda tsabar son kai. Kungiyar zata dade tana fama da radadin wannan gazawar da shuagabannin suka yi a lokacin taron kolin nasu na birnin Brussels, wanda da farkon fari aka yi fatan cewar zai taimaka a samu bakin zaren warware tagwayen matsalolinta da suka hada da na kudi da daftarin tsarin mulki. A yayinda sabbin kasashe goma na kungiyar suka nuna sassauci tare da yin bakin kokarinsu wajen ganin an shawo kan wadannan matsaloli, a nasu bangaren tsaffin kasashen kungiyar sun ci gaba ne da nuna taurin kai, lamarin da ya bata wa shugaban kungiyar P/M kasar Luxemburg Jean-Claude Juncker rai matuka gaya, inda ya ce wannan taurin kai abin kunya ne daga bangaren tsaffin kasashen Kungiyar ta Tarayyar turai. An lura da yadda kwalla ta cika idanun shugaban gwamnatin Jamus lokacin da yake batu a game da wani abin bakin ciki da takaicin da kusan bai taba ganin shigensa ba. Alhakin wannan gazawa ba kawai ya rataya ne a wuyan P/M Birtaniya Tony Blair ba, wanda ya ki yarda da ya janye daga rangwamen kudaden gudummawar da ake wa Birtaniyar. Abin da ya kara rura wutar rikicin shi ne fitowa fili da shuagabannin gwamnatocin kasashen Netherlands da Sweden suka yi suna masu neman da a yi musu rangwamen kudaden gudummawar da suke bayarwa. Kazalika kasashen Faransa da Spain, babu daya daga cikinsu da ta amince ta janbye daga alfarmar da take samu daga baitul-malin kungiyar. Da farkon fari dai an saka dogon buri a game da cewar akalla shuagabannin kasashen kungiyar zasu yi bakin kokarinsu wajen ganin an cimma wata manufa mai sassauci a tsakani a lokacin taron kolin nasu domin share wa jama’a hawaye dangane da rikicin da ya biyo bayan fatali da kasashen Faransa da Netherlands suka yi da daftarin tsarin mulki bai daya na kasashen Turai. Amma sai ga shi murna ta koma ciki, kuma a halin yanzu ba wanda ya san irin alkiblar da za a fuskanta dangane da makomar kungiyar da fafutukar hadin kann Turai ba. Daga zauren taron kolin dai ba wani hasken da aka samu a game da matakin da shuagabannin ke da niyyar dauka domin magance wadannan tagwayen matsaloli da suka hada da maganar kasafin kudi da daftarin tsarin mulki bai daya tsakanin kasashen kungiyar tarayyar Turai.