TARON KOLIN KUNGIYYAR KASASHEN LARABAWA A ALGIERS. | Siyasa | DW | 21.03.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

TARON KOLIN KUNGIYYAR KASASHEN LARABAWA A ALGIERS.

Rahotanni dai da suka iso mana a yanzu haka na nuni da cewa za a gudanar da wan nan taron ne a wani yanki da marigayi tsohon shugaban yankin Palasdinawa,malam Yassir Arafat ya gabatar da jawabin samar da yantacciyar kasa ta Palasdinu shekaru 16 da suka gabata.

Ya zuwa yanzu dai shirye shirye sun kammala tsaf na fara gudanar da wan nan taro mai dimbin tarihi ga kasashen larabawan,game da samun sukunin wanzar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya baki daya.

A lokacin wan nan taro ana kyautata zaton cewa shugabannin kasashen kungiyyar zasu rattaba hannu akan matakin da ministocin harkokin wajen su suka cimma game da samun sulhu a tsakanin kasar israela da sauran kasashen yankin,bisa hujjar samun wanzuwar zaman lafiya a yankin na gabas ta tsakiya baki daya.

Kokarin cimma wan nan mataki dai ya biyo bayan wani daftari ne da kasar Jordan ta gabatar na daukar matakan dai dai ta dangantakar data kwabe a tsakanin kasashen da kuma kasar Israela.

A karkashin wan nan daftari akwai bukatar mahukuntan na israela janye nasu ya nasu daga babakeren da sukayi na iyakokin wasu kasashe a yankin, a matsayin hanya daya ta cimma suklhu a tsakanin juna.

A can baya dai kasar Jordan tayi kokarin ci gaba da gudanar da huldar yau da kullum da mahukuntan na Israela a tun bayan da suka sauko daga matakin da suka hau na daukar ran masu tsattsauran raayi na yankin Palasdinawa.

Haka suma a nasu bangaren kungiyoyin masu tsattsauran raay