1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kolin kungiyyar Eu a Brussels

Shugabannn kungiyyar gamayyar Turai, wato Eu naci gaba da hallara a Birnin Brussels na kasar Belgium don fara taron kolin kungiyyar.

Ajandar taron na wannan lokaci dai shine na cimma matsaya guda game da kasafin kudin kungiyyar na shekaru bakwai masu zuwa a nan gaba.

Ya zuwa yanzu dai kusan shawarar da kasar Biritaniya ta kawo na kokarin warware wannan matsala ya samu suka daga wasu kusoshin kungiyyar na Eu wato kasar Faransa da Jamus.

Wannan dai shawara ta Biritaniya, na bukatar kara yawan kasafin kudin da kungiyyar ke kashewa,wanda hakan zai bada damar karin kudi ga sabbin mambobin kungiyyar, kana a daya hannun kuma da kin rage wani abu daga cikin kason harajin da kungiyyar take mayarwa kasar ta Biritaniya.

Ya zuwa yanzu dai shugabannin kungiyyar ta Eu na daga yanzu izuwa watan maris, su kammala duk wata tattaunnawa da zasu yi don warware wannan takaddama.

Bisa hakan kuwa ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeir cewa yayi matukar ba a cimma matsaya guda ba kafin nan izuwa wannan lokaci to babu shakka hakan ka iya zamewa kungiyyar koma baya.