1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kolin kungiyyar ciniki ta Wto a Hongkong

December 13, 2005
https://p.dw.com/p/BvGY

Taron kwanaki shida na kungiyyar ciniki ta duniya wato, WTO naci gaba da gudana a lardin Hongkong dake kasar Sin.

Babbar ajanda dake gaban wannan taro dai shine na samo bakin zaren warware irin banbance banbance dake akwai ne ta fannin ciniki da kasuwanci a tsakanin kasashe masu tasowa da kuma takwarorin su masu ci gaban masana´antu na duniya.

A cewar bayanai da suka iso mana, mahalarta taron zasu gudanar da tattaunawar tasu ne game da matakan dake kunshe cikin tattaunawar birnin Doha,wanda a wancan lokaci aka tashi daga taron ba tare da an cimma wata matsaya guda ba.

Korafe korafen kasashe masu tasowar dai shine na bukatar ganin an cire duk wasu sarkafe sarkafe dake akwai a harkokin gudanar da ciniki da kuma kasuwancin, musanmamma ta fannin kayan amfanin gona.

A waje daya kuma, rahotanni sun nunar da cewa , masu adawa da hadewar tattalin arziki guri guda, naci gaba da arangama da jamian tsaro a wannan lardi.