TARON KOLIN KUDANCIN KASASHEN ASIA | Siyasa | DW | 02.01.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

TARON KOLIN KUDANCIN KASASHEN ASIA

A yau juma,ane hajji babbar rana ministocin kasashen kudancin nahiyar asiya suka fara gudanar da wani taron kolin duba yiwuwar sasantawa tare da kawo karshen banbance banbancen da kasashen nasu suka fuskanta a baya,tare da kulla yarjejeniyar huldar kasuwanci a tsakanin su ba tare da samun wani cikas ba. Haka kuma a lokacin taron ministocin za kuma su tattauna yiwuwar warware matsalar dake akwai a tsakanin kasasashen yankin na kudancin yankin na Asiya. Wadan nan nan dai kasashe na wannan yanki da akafi samun rashin fahintar juna a tsakanin su sun hadar da kasar India da kuma Pakistan,wadan da dukkannin su kasashe ne da suka mallaki makamin nukiliya na kare dangi. A cewar jami,in hukumar kula da ciniki da kuma kasuwanci na kungiyyar kasashen kudancin yankin na ASiya,Waqar Ahmad Sheik cewa yayi muddin dai aka samu nasarar cimma dai dai to a tsakanin kasasr ta India da kuma Pakistan,musanmamma ta fannin siyasa to babu shakka, wannan nahiya ta kudancin Asiyan zata samu bunkasa ta fannoni daban daban na rayuwar Bil adama. Waqar Ahmad yaci gaba da cewa,dole ne sai an samu taimakon wadan nan kasashe biyu,wannan batu da kungiyyar ta kasasashen kudancin na Asiya tasa a gaba zai samu cimma nasara,musanmamma bisa lakari da cewa Kasashen na India da Pakistan sunfi kowace kasa a yankin karfin tattalin arziki. A yanzu haka dai a cewar rahotanni da suka iso mana,wadan nan kasashe na Pakistan da India sun fara cimma matsaya guda dangane da kulla yarjejeniyar huldatayyar diplomasiyya da kuma safarar abubuwan hawa a tsakanin juna,don samun bunkasar kasuwanci. A kuwa ta bakin sakataren harkokin wajen kasar ta pakistan,Riaz Khokhar,nan bada dadewa ba kasashen biyu zasu bode zirga zirgar hanyoyin jirgin kasa da kuma na sama a tsakanin juna. Ministan harkokin wajen kasar ta Pakistan yaci gaba da cewa da yardar Allah kuma a lokacin wannan taro nasu na yau zasuyi kokarin ganin an cimma yarjejeniyar kasuwanci a tsakanin kasashen na kudancin nahiyar ta Asiya,don a samu damar ci gaba da bude sabon babi naci gaba a fannoni daban daban na rayuwa a wannan yanki na kudancin Asiya baki daya. Bugu da kari,sakatare Riaz ya kuma kara da cewa bisa dukkanin alamu wannan taro zai samu nasarar cimma gaci,bisa la,kari da cewa Faraministan kasar India Atal Behari Vajpayeee ya yarda daya halarci wannan taron kolin ministocin kudancin yankin na Asiya bisa gayyatar mai masaukin baki shugaban kasar Pakistan Pervez Musharraf. Tuni dai shugaba Bush na Amurke ya yabawa wadan nan shuwagabanni biyu na kudancin yankin na Asiya,bisa kokarin da suke na sasasnta rikice rikicen dake tsakanin su,wanda aka shagfe shekara da shekaru ana bugawa. Haka kuma shugaban na Amurka ya kuma kara da cewa yana sa ran a tarurruka na gaba masu zuwa,kasashen biyu zasuyi kokarin ganin sun kawo dukkanin sa in san dake tsakanin su,don samun kwanciyar hankali da kuma ci gaba a fannoni daban daban na rayuwa. Shugaba Bush na Amurka ya kuma cirawa Musharrafat tuta na yadda yake taimakawa wajen yaki da yan taadda da kuma taaddanci a doron kasa baki daya,tare da kiran sauran kasashen duniya dasu bi sahu,don cimma zaman lafiya mai dorewa a fadin duniya baki daya.