1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kolin kasashen Euromed na fuskantar barazanar watsewa

Ana fuskantar barazanar tashi baram-baram a taron kolin kasashen tarayyar Turai EU da takwarorinsu na yankin tekun Bahar Rum saboda takaddama akan ma´anar ta´addanci. Yayin da kungiyar EU ke son ta yi suka da kakkausar harshe akan ayyukan ta´addanci, su kuwa wakilan kasashen Larabawa na son a mayar da hankali ne akan Falasdinawa musamman dangane da ´yancin bijirewa matakan mamaya. Ga sabuwar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel wannan taron wanda za´a fara da yammacin yau a birnin Barcelona zai kasance taron koli na farko da za ta halarta a waje tun bayan darewarta kan kujerar shugabar gwamnatin kasar ta Jamus a ranar talata da ta gabata. Merkel zata gana da FM Spain Jose Luis Rodrigues Zapatero da kuma FM Turkiya Recep Tayyip Erdogan.