Taron Kolin Kasashen ACP a Maputo | Siyasa | DW | 24.06.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron Kolin Kasashen ACP a Maputo

A yau alhamis ne kasashen gamayyar ACP da suka hada da kasashen Afurka da Karibiya da Tekun Pacifik suka fara taron kolinsu na yini biyu a Maputo, fadar mulkin kasar Muzambik a karkashin taken "A hadin kai zamu iya kyautata makomarmu"

A lokacin da take bayani game da taken da aka ba wa taron kolin, P/Mr kasar Muzambik Luiza Diogo ta ce wannan take na mai yin nuni ne da tahakikanin halin da ake ciki a kasashe da dama na gamayyar Afurka, Karibiya da Pacufik, wato ACP a takaice. Wadannan kasashe suna fuskantar kalubala iri dabam-dabam, musamman a game da zaman lafiya da tsaro da kuma kwanciyar hankalinsu. A baya ga haka akwai batutuwan da suka shafi yarjeniyoyin ma’amallar tattalin arziki tsakanin kasashen ACP da na Kungiyar Tarayyar Turai a karkashin kudurorin kungiyar ciniki ta duniya WTO. Ana dai sa ran cewar kasashen dake halartar taron kolin zasu gabatar da wani tsayayyen mataki domin sake farfado da shawarwari tare da kungiyar cinikin ta WTO. Muhimmin abnu shi ne samun cikakken hadin kai tsakanin illahirin kasashen ta yadda zasu iya magana da murya daya a shawarwarinsu da kungiyar WTO. Ainifin abin dake hana ruwa gudu ga wadannan shawarwari dai shi ne maganar karya farashin amfanin noma. Bisa ga ra’ayin kasashen ACP wannan manufa da kasashen yammaci ke tu’ammali da ita, babban cikas ce ga harkokin ciniki tsakanin kasa da kasa. Wannan sabanin shi ne ya haddasa rashin nasarar shawarwarin kungiyar ta WTO da aka gudanar a Mexiko shekarar da ta wuce. Wannan taron, kamar yadda P/Mr kasar Muzambik Luiza Diogo take gani, abu ne da zai ba wa kasashen ACP wata dama ta bitar lamarin a tsanake tare da tantance ire-iren abubuwan da suka faru ta fuskar siyasa da tattalin arziki da zamantakewar jama‘a tun daga taron kolinsu na shekara ta 2002. Hakan abu ne dake da muhimmanci wajen ba wa kungiyar wata tsayayyar alkibla bai daya tsakanin ‚ya’yanta. Yarjejeniyar Cotonou da aka cimma a shekara ta 2000 ita ce ke fayyace ka’idojin ma’amalla tsakanin kasashen ACP da na KTT. Manufar yarjejeniyar kuta ita ce domin rufa wa kasashen ACP baya su samu ikon shiga ana damawa da su sosai da sosai da dangantakar ciniki ta kasa da kasa. A karkashin wannan yarjejeniya kasashen ACP na da ikon shigar da kayayyakinsu kamar ayaba da sukari da kuma auduga a kasuwannin kasashen KTT. To sai dai kuma a halin yanzu kasashen ACP sun damu dangane da sabbin kasashe goma da kungiyar tarayyar Turai ta karbesu karkashin inuwarta saboda mummunan tasirin da lamarin zai yi a dangantakar sassan biyu. Kimanin shuagabannin kasashe 30 ne ake sa ran zasu halarci taron kolin na Maputo, inda a gefen taron kasashe masu karamin karfi na gamayyar ta ACP zasu gana da juna a wawware domin tattaunawa akan cinikin sukari tsakaninsu.