1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kolin kasashe 'yan rabbana ka wadata mu a Mali

June 11, 2007

Kafada-da-kafada da taron kolin G8 an gudanar da taron kasashe 'yan rabbana ka wadata mu a kasar Mali

https://p.dw.com/p/BtvM

Babban abin da mahalarta taron a kasar Mali suka yi korafi akansa dangane da take-taken kasashe masu ci gaban masana’antu shi ne yawanta alkawururruka da suke yi ba tare da sun cika ba. Dounatie Dao daya daga cikin masu alhakin shirya taron na ‘yan rabbana ka wadata mu ya bayyana takaicinsa a game da kasashen G8, wadanda ya ce ko kadan ba su damu da makomar Afurka ba. Dounatie Dao ya kara da cewar:

“Mun gaji da maganganu na fatar baka da ake nanata mana daga shekara zuwa shekara. Maganganu ne na kawai wadanda ana yinsu ne, amma basu da wata ma’ana. An sha zartar da kudurori ba tare da an aiwatar da ko da kwaya daya daga cikinsu ba. Kuduri na baya-bayan nan shi ne maganar yafe basussuka, amma kawo yanzu ba abin da ya faru.”

A taron kolin da kasashen G8 suka gudanar a Gleneagles a shekara ta 2005 ne aka yi alkawarin yafe basussuka da kuma bunkasa yawan kudaden taimakon raya kasa zuwa dala miliyan dubu hamsin a shekara. A kuma wannan taron na Heiligendamm sai aka sake nanata wannan alkawari tare da ikirarin yin kari zuwa dala miliyan dubu sittin domin yakar cuttuka da suka hada da AIDS da zazzabin cizon sauro da tarin fuka. Mahalarta taron na kasashe ‘yan rabbana ka wadata mu a Sikasso ta kasar Mali sun bayyana wannan alkawari tamkar ba’a. Dounatie Dao ya ce:

“Abin da zamu iya cewa game da wannan alkawari shi ne: a yi dai mu gani. Saboda mun gaji da gafara sa bama ganin kaho.”

A taron na Mali an mayar da hankali ne akan matsalolin da suka shafi samar da isasshen abinci da ruwan sha mai tsafta da ilimi da kuma guje-gujen hijira. Sai kuma matsalar cin hanci da ta dade tana ci wa al’umar Afurka tuwo a kwarya. Dao yayi bayani akan wannan matsala yana mai cewar:

“Babu wani misali na kirki da za a iya bayarwa a game da makomar kudaden taimako, saboda galibi ana rub da ciki da su ne. Muddin aka ci gaba akan haka kuwa ba yadda za a yi kasashen Afurka su samu ci gaba, ballantana a yi batu a game da makomar mulkin demokradiyya da girmama hakkin dan-Adam a nahiyar.”

Bisa ga ra’ayin mahalarta taron na Mali ko da yake wajibi ne a rika bin diddigin makomar kudaden taimakon, amma abu mafi a’ala da Afurka ke bukata shi ne kamanta adalci a harkokin ciniki na kasa da kasa da kawance tsakani da Allah.