Taron kolin EU da Latunamirka a Vienna bai cimma wani abin kirki ba | Labarai | DW | 13.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kolin EU da Latunamirka a Vienna bai cimma wani abin kirki ba

Shugabannin kasashen Venezuela da Bolivia sun yi watsi da kiran da KTT ta yi musu na su yi koyi da sauran shugabannin yankin Latunamirka, kana kuma su sassauto daga tsauraran manufofinsu na kuntatawa masu zuba jari na ketare musamman a fannin makashi da cinikaiya. A jiya dai ne aka kammala taron kolin shugabanni 60 da suka hada da shugabannin KTT da takwarorinsu na yankin Latunamirka a birnin Vienna na kasar Austria. Babbar manufar taron dai ita ce cimma wata yarjejeniya akan huldodin cinikaiya. To amma shirin gwamnatin Bolivia na mayar da kamfanonin mai na ketare mallakin gwamnati shi ne ya mamaye zauren taron.