Taron kolin Au ya dauki dumi game da neman shugaba na gaba | Labarai | DW | 23.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kolin Au ya dauki dumi game da neman shugaba na gaba

Rahotanni daga birnin Khartoum na kasar Sudan na nuni da cewa batun kasar da zata shugaban ci kungiyyar Au ne a tsawon wa´adin shekara guda ne yafi daukar hankali a lokacin taron na wuni biyu.

Bisa al´ada dai duk kasar da take daukar bakuncin taron itace take karbar ragamar shugabancin kungiyyar na karba karba.

Rahotanni dai sun nunar da cewa kasar Sudan da shugabannin kungiyyar 53 ke shirin bawa shugabancin kungiyyar, tuni ta fuskanci kakkausar suka daga kungiyoyin kare hakkil bil adama, na ingiza wutar rikice rikice a yankin Darfur na kasar.

Da yawa dai daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil adaman sun kuma shaidarwa shugabannin na Au cewa, bawa kasar ta Sudan wannan mukami ka iya dakushe kima da darajar kungiyyar a idon duniya , bisa irin take hakkin bil adaman dake ci gaba da wanzuwa a yankin Darfur.

Ya zuwa yanzu dai tuni shugabanni biyar daga cikin shugabannin na Au suka bukaci , Shugaba Omar El Bashir na Sudan daya janye bukatar sa ta neman wannan shugabanci.