1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kolin Afirka da Faransa a birnin Bamako na Mali

December 3, 2005
https://p.dw.com/p/BvIF

Shugabanin kasashen Afirka sun hallara a Bamako babban birnin Mali don gudanar da wani taron yini biyu da ake sa rai zai mayar da hankali akan rikice-rikice da kuma matsalolin iri dabam-dabam da matasan wannan nahiya ke fuskanta. A jiya juma´a shugaban Mali Amadou Toumani Toure,wanda kasar ke karbar bakoncin taron Afirka da Faransa na karo 23 ya tarbi shugaba Jaques Chirac lokacin da ya isa birnin na Bamako. Rikicin da ake fama da shi a lardin Darfur na Sudan da kuma yakin basasan da ya raba kasar Ivory Coast gida biyu da matsalolin da suka yiwa matasan nahiyar Afirka katutu, zasu mamaye ajandar wannan taro. Wani rahoto da ofishin MDD a Senegal ya bayar a ranar alhamis ya nunar da cewa kimanin kashi 75 cikin 100 na matasan nahiyar Afirka ´yan kasa da shekaru 30 na haihuwa ba su da aikin yi.