Taron koli na shugabannin Kungiyar EU. | Siyasa | DW | 27.10.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron koli na shugabannin Kungiyar EU.

Shugaban gwamnatin tarayyar Jamus mai barin gado, Gerhard Schröder, ya kare matsayinsa na bin tsarin harkokin kasuwanci na cakuda salon gurguzu da na jari-hujja. Shugaban ya bayyana hakan ne a wani taron yini daya da shugabannin kasashen Kungiyar Hadin Kan Turai suka yi a Hampton Court kusa da birnin London a ran alhamis.

Shugabannin kasashen Kungiyar Hadin Kan Turai gaban gun taronsu a fadar Hampton Court kusa da birnin London.

Shugabannin kasashen Kungiyar Hadin Kan Turai gaban gun taronsu a fadar Hampton Court kusa da birnin London.

A taron kolin yini daya da shugabannin kasashe 25 na kungiyar Hadin Kan Turai suka yi a Hampton Court a birnin London, shugaban gwamnatin Jamus mai barin gado, Gerhard Schröder, ya yi gargadin cewa, bai kamata Turai ta bi misalin Birtaniya wajen tsara manufofin tattalin arzikinta ba. Shirin sassauta harkokin ciniki da Birtaniyan ke bi, ba abin kwaikwayo ba ne, saboda duk wani yunkurin bunkasa ciniki, amma wanda ke janyo tabarbarewar halin rayuwar jam’a, ba abin a zo a gani ba ne, kuma hakan ba ya janyo ko wace fa’ida, inji Schröder. Ya kara da cewa:-

„A nawa ganin dai, shirye-shirye daban-daban na bin tsarin harkokin kasuwanci na cakuda salon gurguzu da jari-hujja, su ne suka fi dace wa Turai. Kuma abin da muke karfafawa a nan ke nan“.

A nasa bangaren, Firamiyan Birtaniya Tony Blair, wanda kasarsa ce ke shugabancin kungiyar Hadin Kan Turan a halin yanzu, ya yi kira ga yi wa tsarin tafiyad da harkokin kungiyar garambawul, don kago sabbin hanyoyi na kula da al’umman kasashen nahiyar, wadanda suke ta kara tsufa. Bugu da kari kuma, ya bayyana cewa, ba za a iya zaman ba ruwanmu ana ganin yawan marasa aikin yi na ta habaka a kasashen kungiyar ba. A halin yanzu dai, an kiyasci cewa, kusan mutane miliyan 19 na kasashe mambobin kungiyar ne ba su da aikin yi.

Firamiyan na Birtaniya, da shugaban Hukumar kungiyar Hadin Kan Turan, José Manuel Barroso sun kuma gabatad da wani shiri mai dauke da jigajigai guda 5, wanda ke da burin bunkasa ilimi da binciken kimiyya, da kau da shingen kasuwanci a duk kasashen kungiyar. Har ila yau dai shugabannin biyu sun kara da cewa, za a kafa wani asusu kuma, wanda zai dinga bai wa mutanen da suka rasa guraban aikinsu sakamakon aiwatad da shirin nan na hadayyar tattalin arziki ko kuma Globalisation, tallafi. A karo na farko kuma Tony Blair ya nuna goyon bayansa ga shirin nan da ake ta korafi a kansa, na daidaita tsarin karbar haraji da na samad da makamashi.

Shugaban gwamnatin Jamus mai barin gado, Gerhard Schröder, shi ma ya yi kira ga kara yawan kudin da kungiyar za ta kashe kann ilimi da binciken kimiyya zuwa kashi 3 cikin dari, na kudaden shigar da suka samu daga cinikayyar cikin gida, a ko wace shekara. To sai dai, a taron na yau, shawarwari kawai aka yi ta bayarwa. Babu wani kudurin da aka zartar. Game da hakan dai, shugaba Schröder ya bayyana cewa:-

„Ba mu dai zartad da wani kuduri ba. Abin da muka tattauna a kai shi ne, ina Turai z ata mai da alkiblar ta ? Za mu mai da hankalinmu kan kasuwanci ne kawai, ko kuwa, al’ummominmu na fatar samun wasu ababan daban kuma ?“

Game da rashin jtuwar da ake samu tsakanin mambobin kungiyar dangane da kasafin kudinta na shekara 2007 zuwa 2013 kuwa, shugaba Schrödern ya ce kasarsa ba za ta nuna wani sassauci ba kuma a kan matsayin da ta dauka. Ya karfafa cewa, ko bayansa ma, sabuwar gwamnatin Jamus ba za ta kauce daga wannan matsayin ba.

Rikicin dai ya fi tsamari ne tsakanin Faransa da Birtaniya, inda ita Birtaniyan ke nuna cewa ba ta da shirin tattaunawa ma kan batun rage tallaffin da take samu daga kungiyar, muddin Faransa ba ta sakar wa asusun kungiyar duk tallafin da manomanta ke samu ba. Kai tsaye ne dai shugaba Chirac ya yi watsi da wannan shawarar.

Daga baya dai, Firamiyan Birtaniyan, Tony Blair, ya nemi sulhunta rikicin, inda ya bayyana cewa:-

„Kamata ya yi dai Birtaniya da Faransa su sami hadin kai, a duk inda hakan zai yiwu. Babu shakka muna da bambancin ra’ayi. Amma Turai ba z ata iya ci gaba ba, sai mun cim ma wata madafa ta bai daya. Abin da muke yunkurin cim ma kuma ke nan.“

 • Kwanan wata 27.10.2005
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu4Y
 • Kwanan wata 27.10.2005
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu4Y