TARON KOLI NA KASASHEN ASIYA DA AFIRKA A KASAR INDONESIYA. | Siyasa | DW | 25.04.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

TARON KOLI NA KASASHEN ASIYA DA AFIRKA A KASAR INDONESIYA.

A karshen makon da ya gabata ne aka kammala taron koli na yini biyu, na kasashen Asiya da Afirka a birnin Jakarta na kasar Indonesiya. Rikicin da ya barke tsakanin kasashen Sin da Japan, ya kusan mamaye duk wasu shagulgula na taron.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan da Firamiyan Japan Koizumi a taron koli na kasashen Asiya da Afirka da aka yi a kasar Indonesiya.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan da Firamiyan Japan Koizumi a taron koli na kasashen Asiya da Afirka da aka yi a kasar Indonesiya.

A lokacin habakar yakin cacar baka, tun da shekaru 50 da suka wuce ne, shugabannin kasashen Sin da Indiya da Indonesiya, wato Zhou Enlai, da Jawarhal Nehru da kuma Sukarno, suka kira wani taron koli na kasashe masu tasowa daga nahiyar Asiyan da Afirka, inda suka kafa tubalin abin da ya zamo rukunin nan na kasashen `yan ba ruwanmu. A wannan lokacin, fiye da rabin kasashen da suka tura wakilansu zuwa taron, ba su da `yanci ko kuma, ba su cikin Majalisar dinkin Duniya. A yau kuwa, duk kasashen, mambobin Majalisar ne ta dinikin duniyar.

Amma duk da hakan, canje-canjen da aka samu a harkokin siyasar duniya, musamman ma dai bayan shigowar salon na na hadayya, wanda aka fi sani da suna Globalisation a turance, sun janyo hauhawar tsamari, sakamakon barkewar sabbin halayya na kishin kasa da sósùwar rai tsakanin wasu kasashen rukunin, kamar yadda ake ta fama da shi a halin yanzu tsakanin kasashen Sin da Japan. A gun taron kolin da aka yi a birnin Jakarta a karshen makon da ya gabata dai, batun huldodi tsakanin kasashen biyu ne, ya kusa jan hankullan kafofin yada labarai daga ainihin gundarin taron ma gaba daya. Kowa dai ya sa ido ne kan shugabanni biyu, wato shugaban Hu Jintao na Sin da kuma Firamiyan Japan Junichiro Koizumi . An dai yi ta yada rade-radi, game da saduwarsu ko kuma kaucewarsu ga juna a gun taron. A karshe dai sun gana da juna, suka kuma bayyana tare, a wani taron maneman labaran da suka kira inda suka bayyana shirinsu na warware duk rikicin da ke tsakaninsu ta hanyar tuntubar juna.

Rashin jituwa tsakanin kasashen biyu, na da asali ne daga wani tsohon rikici da suka dade suna ta fama da shi. Ita dai Sin na sukar Japan ne, da kokarin dakusad da da kaifin wani shafi na tarihinta a lokacin yakin duinya na biyu, inda dakarunta suka gallaza wa sauran al’umman yankin kudu maso yammacin Asiya. Tana kokarin shafe wannan babin ne daga tarihinta, abin da Sin ke ganin cewa ko kadan bai dace ba. daya misali a nan dai, shi ne wani littafin tarihi da aka buga a kasar ta Japan, wanda ke kaucewa daga sukar danyen aikin da dakarun Japan din suka gudanar a loakcin yakin duniyar, na biyu. Hakan dai ya janyo barkewar jerin zanga-zanga da aka yi ta yi a kasar Sin, inda a wasu lokutan ma suka kai ga tashe-tashen hankulla.

A nata bangaren , Japan ta zargi Sin ne da yin amfani da wannan zanga-zangar, wajen shimfida mata surkuki da kaya, a yunkurin da take yi na samun kujerar dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar dinkin Duniya. Amma game da wannan sukar Sin ba ta mai da martani ba. Ta bar wa kasashen yankin ne, nauyin bayyana ra’ayoyinsu a kan wannan batun. Ta hakan ne kuwa, gidan talabijin din kasar, a cikin wani rahotonsa, ya ari bakin ministan harkokin wajen kasar Korea Ta Kudu, a jawabin da ya yi wa taron kolin kasashen Afirka da na Asiyan, yana mai cewar " karfin tattalin arziki kawai, bai isa ba, wajen bai wa wata kasa, cancantar samun kujerar dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar dinkin Duniya. Kamata ya yi, kasar da ke fafutukar kai ga wannan matsayin, ta kuma ba da tata gudummuwa wajen samad da zaman lafiya a duniya baki daya." Ko wane dan kasar Sin dai, ya san kasar da ministan ke matashiya da ita a cikin jawabinsa.

A huskar tattalin arziki kuwa, kasashen biyu masu hamayya da juna a nahiyar Asiya, wato Sin da Japan, suna da nasaba da juna sosai, ta yadda babu wani daga cikinsu da ke sha’awar ganin cewa, an sami raunana mai dorewa a huldodin da ke tsakaninsu. Idan aka dubi lamarin ta wannan bangaren, za a ga cewa shugaba Hu da Firamiya Koizumi, ba su da wani zabi, illa su yi hangen nesa inda kuma za su karfafa al’adar nan ta kyakyawar dangantaka tsakanin al’ummomin kasashen biyu.

Ko lalle ne al’ummomin wadannan kasashen na yi wa lamarin kallon da shugabanninsu ke yi ? Babu dai tabbas kan hakan. A halin yanzu dai, ana hasashen cewa zanga-zangar da ta barke a kasar Sin, za ta kai kololuwarta ne a ran 4 ga watan gobe. Saboda wannan ranar, ita ce ranar cika shekaru 14 da farkon zanga-zangar neman dimukradiyyar nan da da daliban kasar Sin din suka yi a dandalin Tiananmen, a cikin shekarar 1991. A wannan lokacin ma, daliban sun nuna matukar adawarsu n e ga yunkurin yada angizonta a duk yankin Asiyan da Japan ke yi.

Wannan rikici tsakanin Sin da Japan dai, ya kusa mamaye makasudin taron kolin na nahiyar Afirka da Asiya. Duk da hakan dai, nahiyoyin, sun cim cim ma burin mika hannun abokantaka ga juna a karo na biyu. Amma ba sai an jira har bayan wasu shekaru 50 ba kuma, kafin a yi wani taron koli tsakanin kasashen Afirka da na Asiyan. Duk mahalarta taron na Jakarta dai sun yi amanna da shawarar gudanar da wannan taron a duk shekaru 4-4 nan gaba. A cikin jawabin bayan taron da kasashen suka bayar kuma, sun amince da bude wani sabon babi a huldodin dangantaka tsakanin Asiya da Afirka. Cim ma nasarar wannan manufar dai, zai dogara ne kan yadda al’amura za su kasance a yankin kudu maso gabashin Asiya.

 • Kwanan wata 25.04.2005
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvcJ
 • Kwanan wata 25.04.2005
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvcJ