Taron kasuwanci na ƙungiyar D8 a Abuja | Labarai | DW | 08.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kasuwanci na ƙungiyar D8 a Abuja

Ƙasashen dake da mafi rinjayen musulmai a duniya za su kyautata cinikayya a tsakanin su

default

Ƙasashe takwas da ke da mafi rinjayen al'ummar musulmmai a duniya, waɗanda suka haɗa da Nijeriya da Iran da kuma Pakistan sun bayyana burin cimma yarjejeniyar da ta shafi cinikayya a tsakanin su nan da shekara mai zuwa, da nufin riɓanya haɗin kai ta fuskar tattalin arziƙi a tsakanin su.

Ƙasashen da ake yiwa laƙabi da ƙungiyar ƙasashe takwas da tattalin arziƙin su ke tasowa ko kuma D8, sun haɗa da Nijeriya, Iran, Bangladesh, da Masar da kuma Indonisia. Sauran su ne Malaysia da Turkiyya da kuma Pakistan, waɗanda ke gudanar da taron su a Abuja - fadar gwamnatin Nijeriya domin bunƙasa kasuwanci a tsakanin su da kuma rage yawan tarnaƙin dake tsakanin su ta fuskar cinikayya.

A jawabin da ya yiwa shugabannin ƙasashe mambobin ƙungiyar da ke halartar taron, shugaban Nijeriya kana mai masaukin baƙi Dakta Goodluck Ebele Jonathan ya ce ko da shike gwamnati ce za ta taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasar tattalin arziƙi, amma ɓangaren 'yan kasuwa masu zaman kansu ne za su kasance ja gaba a cikin shirin. Cinikayya a tsakanin ƙasashen ƙungiyar ta D8, wadda aka samar a shekara ta 1997 da nufin inganta harkokin tattalin arziƙi dai, ƙiyasi ya nunar da cewar ta kai na kuɗi dalar Amirka miliyan dubu 68, wanda ya zo dai dai da kashi ukku cikin 100 na harkokin cnikayya a duniya baki ɗaya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu