1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kasashen makwabtan Iraƙi akan al´amuran tsaro a kasar

A wani lokaci yau wakilai daga kasashe da kungiyoyi 16 zasu tattauna a Bagadaza don neman mafita daga jerin tashe tashen hankula da rashin tsaro a Iraqi. Daga cikin mahalarta taron inda za´a tattauna kan al´amuran tsaro a Iraqi, akwai jami´an diplomasiya na makwabtan kasar da na kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD. A karon farko taron zai ba da damar zama kan teburi guda tsakanin wakilan Amirka da na Iran da kuma na Syria. FM Iraqi Nuri Al-Maliki ya bayyana haka da cewa wata alama ce ta samar da zaman lafiya a kasar sa. To amma ministan harkokin waje Hoshiyar Sebari ya ce taron kadai ba zai warware matsalolin kasar ba. A wani labarin kuma dakarun gwamnatin Iraqi sun ce sun kame shugaban wata kungiyar ´yan takife ta ´yan sunni a yammacin birnin Bagadaza. Gidan telebijin Iraqi ta bayyana wannan mutumin da Abu Omar al-Baghdadi, wanda aka yi imani cewar shi ne jagoran wata kungiyar ´yan tawaye dake kiran kanta kasar Islamiya ta Iraqi.