Taron kasashen larabawa | Labarai | DW | 29.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kasashen larabawa

Shugabannin kasashen larabawa sun shiga kwana na biyu na babban taron kolinsu inbda ake sa ran a yau din ne zasu sake kaddamar da da shirin zaman lafiya na yankin gabas ta tsakiya.

Wannan shiri dai yayiwa Israila tayin zaman lafiya tsakaninta da dukkan kasashen larabawa idan ta janye daga dukkan yakuna data mamaye a lokacin yakin 1967.

Ya kuma yi kira ga kafa kasar Palasdinu mai yanci tare da maido da yan gudun hijira Palasdinwa.

Shekaru 5 da suka shige Israila tayi watsi da wannan tayin,amma masu lura da alamura sunce akwai alamun cewa a wannan karo Israilan zata maida martani mai muhimmanci.