Taron kasashen duniya kan Libanon a birnin Rom | Labarai | DW | 26.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kasashen duniya kan Libanon a birnin Rom

An kammala taron kasashen duniya akan Libanon a birnin Rom na Italiya a daidai lokacin da ake kara matsa lamba na cimma tsagaita wuta tsakanin Isra´ila da dakarun Hisbollah. Manyan jami´an diplomasiya daga Amirka, yankin GTT da nahiyar Turai sun tattauna domin gano hanyoyin tura kayan taimakon jin kai cikin gaggawa zuwa Libanon, inda fararen hula kimanin dubu 500 suka tsere daga gidajensu. Shugabannin kasahen Larabawa sun nuna bukatar samar da wani shirin zaman lafiya na gaggawa, to amma Amirka ta ce halin da ake ciki yanzu ba zai sa a samar da wani shirin tsagaita wuta mai dorewa ba. A lokacin da ya ke tofa albarkacin bakinsa game da taron kan rikicin na Lebanon, FM Italiya Romano Prodi ya ce an gudanar da taron na birnin Rom akan manufofi guda 3. Ba´a dai gayyaci Isra´ila da Hisbollah da kuma Syria a wannan taro ba.