Taron kasashen dunia a game da kafofin sadarwa a Tunis | Labarai | DW | 16.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kasashen dunia a game da kafofin sadarwa a Tunis

A birninTunis na kasar Tunisia, an buda babban taron kafofi sadarwa masu taka rawa zamani a dunia.

Wakillai daga kasashe 170 da su ka zo daga sassa daban daban, bisa gayyatar Majalisar Dinki Dunia, za su masanyar ra´ayoyi, a game da banbance- banbance, ci gaban da ke akwai ta fannin, kafofin sadarwa na Internet, tsakanin kasashe masu karfin tattalin arziki, da kasashe matalauta da masu tassowa.

Shugaban kasar Tunisia ne ,Zine Al Abedin Ben Ali, ya kaddamar da wannan biki, tare da halartar sakatara Janar na Majalisar Dinkin Dunia, Koffi Annan, da shugabanin kasashe kimanin 20 na Afrika, da gabas ta tsakiya.

A cikin jawabin da yayi, Ben Ali yayi fatan daga yanzu a sake lalle ta yada kasashen baki daya za su moriyar ci gaba da aka samu ta fannin kafafofin sadarwa na zamani.

Shi ma Koffi Annan, ya gabatar da bukatar Majalisar Dinkin Dunia, ta cimma wannan buri.