Taron Kasashen AU da na EU a Rabat | Siyasa | DW | 12.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron Kasashen AU da na EU a Rabat

Tare da wani kudurin shawo kan matsalar bakin haure aka kammala taron kasashen AU da na EU a Rabat ta kasar Maroko

default

Dukkan mahalarta taron bitar matsalar ta bakin haure a birnin Rabat sun amince cewar wajibi ne sakamakon taron ya haifar da wani da mai ido akan manufa. Sanarwar bayan taron dai ta kunshi wasu matakai ne guda biyu wadanda suka hada da manufofin tsaro da taimakon raya kasa. Wannan babban ci gaba ne aka samu idan an kwatanta da yadda al’amura suka kasance a zamanin baya in ji ministan cikin gida na kasar Senegal Ousman Ngom:

“Bai kamata a yanzun tarukan da zasu baya su kasance akan kayyade yawan bakin haure kawai ba. Muhimmin abu a gare mu a yanzu shi ne a mayar da hankali ga dukkan matsalolin na bakin haure da raya makomar kasashen Afurka. Wannan shi ne abin da za a bayar da la’akari da shi a cikin wannan karnin da muke ciki.”

Wakilan kasashen Turai dai sun so taron ya ba da la’akari ne kacokam akan batutuwan tsaro tare da kasashen da bakin hauren ke fitowa da kuma wadanda suke bi ta kansu domin shigowa Turai. Wannan maganar ta shafi har da sake karbar bakin hauren da akan komar da su gida. Wannan maganar an dade ana sabani kanta tsakanin kasashen Turai da na Afurka. Amma ainifin maganar ta shafi hadin kai ne tsakanin sassan biyu domin karya alkadarin ‘yan baranda masu fataucin ‘yan Adam da kuma tsaron iyakokin kasashen kungiyar tarayyar Turai. Ga dai abin da mataimakin ministan harkokin wajen Ghana Ossei Ajei yake cewar:

“Abin da zan fadi shi ne, duk wani mataki na shingence iyakoki domin hana shigowar mutane ba zai yi karko ba. Abu mafi alheri shi ne bin diddigin matsalar daga tushenta. Shin me ke haddasa kaurace-kauracen mutanen, kuma wadanne irin mutane ne ke barin kasashensu. Idan mun ba da la’akari da haka zamu iya shawo kan matsalar. A hakika kuwa akwai matsaloli masu yawa da wajibi ne mu shawo kansu.”

An kuwa saurari wannan kara aka kuma shigar da ita a sanarwar bayan taron da kuma alkawururrukan da kasashen Turai suka yi na ba da taimako. Kasashen na Turai na da niyyar bai wa daliban da ake yayewa daga makarantun sakandare a kasashen Afurka wata dama da ci gaba da karatu a jami’o’insu. Kazalika sun da niyyar rage yawan ladar da ake karba daga kudaden da ‘yan Afurka ke aikawa zuwa gida. Kazalika kasashen na Turai sun yi alkawarin kara yawan kudaden taimakon raya kasashen Afurka.