Taron kasashen Asiya da Pacific | Labarai | DW | 13.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kasashen Asiya da Pacific

Shugabannin Asiya da Pacific na duba cigaban hadin gwiwar tattalin arziki a tsakanin kasashen yankin

default

Shugaban Amirka Barack Obama da Firaministan Japan Naoto Kan a wajen taron APEC

Shugabannin kasashen yankin Pacific guda 21 sun hallara a birnin Yokohama na kasar Japan domin gudanar da taron shekara shekara na hadin gwaiwar tattalin arzikin kasashen nahiyar Asiya da na yankin pacific. Shugaba Barack Obama da shugaban Hu Jintao na China da sauran shugabannin dake halartar taron na sa ran cimma daideto akan  daukar matakin kara samar da walwalar ciniki a yankin na pacific. Kasawar da Obama ya yi wajen cimma  yarajejeniar kasuwanci tsakanin kasarsa da Koriya ta Kudu da kuma kin rukunnin kasashen G20 na biye wa Amirka game da sukan da take wa China akan darajar kundinta, sun bayyanar da raguwar ikon fada a ji da Amirka ke da shi a wannan yanki bisa  lamuran da suka shafi tattalin arziki.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita          : Abdullahi Tanko Bala