1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kasashen Afrika da Faransa.

Hauwa Abubakar AjejeFebruary 15, 2007

A yau ne aka bude taron yini biyu na kasashen Afrika da Faransa a birnin Cannes na kasar ta Faransa inda shugaba Chirac da Angela Merkel suka bukaci shugabannin Afrika da suyi aiki tare wajen ganin an kawo karshen tashe tashen hankula a nahiyar.

https://p.dw.com/p/BtwD
Chirac da Merkel
Chirac da MerkelHoto: AP

Taron na kasar Faransa ya fi mayarda hankali ne wajen nemo hanyoyin kawo karshen rikici a nahiyar Afrika,inda shugaban Faransa J.Chirac ya yi kira musamman ga kasar Sudan da kungiyoyin yan tawaye dasu amince da dakarun Majalisar Dinkin Duniya a yankin Darfur.

Sai dai kuma Alexender Stroh na cibiyar nazarin harakokin Afrika a jamiar Hamburg dake nan Jamus yace manufar taron don duba moriyar albarkatun da Allah ya horewa nahiyar ce.yace:-

“ina ganin muhiman batutuwa 3 ne,wadanda suka hada da danyun albarkatu na Afrika,da matsayin afrika a duniya tare kuma da batun fasahar yada labarai,amma bana ganin cewa wadannan taruka sune hanyoyin magance matsaloli Afrika,sai dai zasu iya kasancewa daya daga cikin hanyoyin da zaa iya cimma nasara”

Kimanin shugabanin Afrika 30 ne da kuma Angela Merkel shugabar gwamnatin jamus wadda ke rike da shugabancin EU suke halartar taron.

A jawabinta Merkel tace Kungiyar Taraiyar Turai zata gaiyaci kasashen Afrika wajen wani babban taro a tsakiyar wannan shekara a kasar Portugal wadda zata gaji kasar a shugabancin Kungiyar Taraiyar Turai.

Merkel tayi kira ga kasashe makwabtan Zimbabwe da su kara matsawa shugaba Robert Mugabe lamba domin a kawo karshen wahalhalu da jamaar kasar suka samu kansu ciki sakamakon manufofinsa.

Merkel tace abin takaici ne yadda Mugabe yake musgunawa abokan hamaiyarsa,da barazan ga manoma tare da lalata gidajen talakaw ba bisa kaida ba.

Kasar ta Zimbabwe dai taki halartar taron nay au saboda kasar Faransa ta nemi wani dabam ya wakilci kasar a madadin shugaba Mugabe,wanda aka dorawa takunkumi ziyara zuwa kasashen EU saboda take hakkin bil adama a kasarsa.

Hakazalika shugaban Afrika ta kudu Thabo Mbeki da takwaransa na Ivory Coast Laurent Gbagbo suma basu halarci wannan taro ba.

Duk da haka dai an samu wakilcin kasashe 48 cikin kasashe 53 na nahiyar Afrika,yawancinsu shugababnin kasashe da suka zo ban kwana ga Chirac,wanda ya dade yana renon dangantaka tsakanin Faransa da kasashen da tayiwa mulkin mallaka a nahiyar.

Kodayake wannan dangantaka tana fuskantar barazana daga kungiyoyi dabam daban na cikin gida dama hulda ta cinikaiya musamman daga bangaren Amurka da China.