1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kasashen Afirka da na Turai a birnin Triplolis akan bakin haure

November 22, 2006
https://p.dw.com/p/Buar
Wakilai na kasashen Afirka da takwarorinsu na kasashen KTT zasu yiwa wani taro a babban birnin kasar Libya da zumar gano hanyoyin yaki da bakin haure. A lokaci daya kuma mahalarta taron zasu yi kokarin cimma manufa ta bai daya da ta shafi shige da ficen baki, wadda kuma zata duba bukatun kasashen da bakin suka fito da kasashe da suke ratsawa ciki da kuma inda suka dosa. Libya dai na daya daga cikin kasashen da bakin hauren musamman daga Afirka ke bi ta ciki suna shiga Turai ta barauniyar hanya ko kuma ta hanyoyi masu hadari. Ministan harkokin cikin gidan Jamus Wolfgang Schäuble ke jagorantar tawagar Jamus a taron.